An samu tsohon dan wasan Najeriya da laifin sayar da wasa a Sweden

Dickson Etuhu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dickson Etuhu ya taka wa Najeriya leda a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka da kuma Gasar Cin Kofin Duniya

Etuhu, wanda ya taba bugawa kungiyoyin Ingila ciki har da Manchester City da Sunderland da Preston da Blackburn da kuma Fulham wasa, ya kaucewa dauri amma sai aka ci shi tara da kuma hukunci jeka-gyara halinka.

Sai dai ba a yi karin haske ba bayan hakan.

Kotun daukaka kara a Stockholm ta ce a bayyane yake Etuhu da wani tsohon dan wasan da ba a ambaci sunan ba, sun yi kokarin shawo kan golan kungiyar AIK Kyriakos Kenny Stamatopoulos da ya sayar da wasan kungiyar a babban wasan rukuni na daya a Sweden a shekarar 2017.

Mai shekara 37, wanda ya bar AIK Solna a shekarar 2016, ya ce zai daukaka kara kan hukuncin a Kotun Koli.

Kotun ta ce "bayanan abin da 'yan wasan suka mikawa dan wasan Stamatopoulos a bayyane sun aikata laifin cin hanci da rashawa.

A cewar kotun tsohon dan wasan ya aikata babban laifi a kasar.

Etuhu ya buga wa Super Eagles wasa sau 20 ciki har da wasannin da ya yi wa kungiyar a Gasar Cin Kofin nahiyar Afirka a 2008 da 2010 da kuma Kofin Duniya a Afirka ta Kudu.