Fifa ta bai wa Arsene Wenger babban mukami

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger zai dawo harkokin wasan kwallon kafa bayan da ya amince ya karbi wani sabon mukami da hukumar kwallon kafa ta duniya (Fifa) ta ba shi wato babban mai kula da ci gaban kwallon kafa a duniya.
Wannan matakin ya kawo karshen jita-jitar da ke cewa tsohon kocin, mai shekara 70, zai koma jagorancin kungiyar Bayern Munich a kasar Jamus.
Wenger ya bar Arsenal ne a watan Mayun shekarar 2018, bayan ya shafe shekara 22 yana jagorancin kungiyar, inda sau uku yana lashe kofunan Premier da kuma kofunan FA bakwai.
"A shirye nake na fara wannan babban aiki mai cike da kalubale," in ji shi.
Sabon mukamin na Wenger zai taimaka wa hukumar Fifa wajen bunkasa wasannin maza da na mata da kuma sauran harkokin da suka shafi kwallon kafa.






