Shin ina dan wasan tsakiyar Arsenal Mesut Ozil yake?

Mesut Ozil

Asalin hoton, Getty Images

Ko ina Mesut Ozil yake yanzu haka?

Wannan wata tambaya ce da dole kocin Arsenal, Unai Emery, ya kosa da amsa ta.

Ozil ya buga wasa daya ne kacal a farkon wasannin gasar Premier ta bana, kuma ba a kara ganin sa ba a wasannin kungiyar guda hudu da ta buga.

A ranar Litinin, lokacin da Arsenal din ta buga wasa da Sheffield United, ba a ga Mesut Ozil ba abin da ya kara sa magoya baya ci gaba da tambaya.

Da sashen BBC na wasanni ya tambayi kocin Arsenal, Unai Emery cewa ko ina Ozil yake a lokacin wasan da Arsenal din ta kwashi kashinta a hannu, sai ya ce, "E zai iya taimaka mana."

Wannan dai ita ce tambayar da ke bakin mutane da dama.

Shin ko Arsenal na kewar Ozil?

Alkaluma ne za su nuna ko Arsenal na kewar Ozil ko a'a.

Tun dai lokacin da Ozil ya fara taka leda a Arsenal, ba a samu wani dan wasa ba da yake da sa a kamar shi. Zancen gaskiya ma babu wanda yake kusa da shi ma.

Mesut Ozil ne babban mai taimaka wa 'yan wasa su ci wasa a wasanni uku na kakar wasannin Premier shida da suka gabata, duk da cewa sunansa bai fito ba a jerin sunaye uku manya a baya.