Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Madrid Derby: Wasa ya tashi canjaras
Atletico Madrid ba ta iya karya kwarin Real Madrid ba na wasa bakwai a La Liga ba tare da rashin nasara ba bayan wasan hamayyar Madrid ya tashi 0-0 a filin wasa na Wanda Metropolitano.
Atletico ba ta jarraba Thibaut Courtois da kyau ba a tsawon minti 90 na wasan duk da cewa sun kai hare-hare amma marasa hadari.
Tawagar Diego Simone ta yi kacakaca da ta Zidane da ci 7-3 a America gabanin fara La Liga ta bana.
Amma wasan yau dari-dari aka rika yin sa, inda mummunan hari biyu kawai aka kai a minti 45 na farko kuma Tony Kroos na Real Madrid ne ya kai su baki daya.
Real ce dai ta rike kwallo mafi yawa a wasan da kashi 56% Atletico kuma 44%, yayin da tawagar Zinedine ta ci gaba da kasancewa a saman teburi da maki 15.
Maki daya ne kacal tsakaninta da Granada da Atletico wadanda ke mataki na biyu da na uku, inda suka bar Barcelona a mataki na hudu da maki 14 bayan ta ci wasan waje na farko a La Ligar bana.
Wannan ne wasa na uku a jere da Real Madrid ta yi ba a zura mata kwallo ba a karkashin Zinedine Zidane.