Inter Milan: Sanchez ya ci kwallon farko sai kuma aka kore shi

Alexis Sanchez ya ci kwallonsa ta farko a Inter Milan kuma alkalin wasa ya kore shi daga fili bayan samun katin gargadi na biyu.

Sanchez wanda ya koma Inter daga Man United a farkon kakar bana a matsayin aro, ya ci kwallon da Sensi ya dada bayan an tare ta, minti biyu bayan Sensi din ya ci ta farko.

Sai dai ya karbi katin gargadi a karo na biyu minti daya bayan dawowa daga hutun rabin lokaci bayan ya fadi da gangan a cikin yadi na 18 - yana neman finareti.

Jakub Jankto ya farke guda daya amma Roberto Gagliardini ya kara ta uku, abin da ya kawo Inter din wasa shida ba tare da rashin nasara ba.

Inter Milan ta ci gaba da zama a saman teburi da makinta 18, maki biyu tsakaninta Juventus wadda take matsayi na biyu.