Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Juventus vs SPAL: Ronaldo ya ci kwallo
Cristiano Ronaldo ya dawo daga jinya da zafi-zafinsa yayin da zakarun Serie A Juventus suka ci gaba da jan zarensu bayan ta doke SPAL.
Ronaldo bai buga wasan da Juve ta lallasa Brescia ba saboda rauni, amma ya ci kwallon ta yau da ka bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Miralem Pjanic ne ya fara sanya Juve a gaba da kwallon da ya dada mai kayatarwa ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.
Mai tsaron ragar SPAL, Etrit Berisha, ya kare ragarsa da kyau bayan ya haramta wa Aaron Ramsey da Sami Khedira jefa kwallon da kowannensu ya kusa ci da ka.
A gefe guda kuma, gwarzon mai tsaron raga Gianluigi Buffon, mai shekara 41 ya buga wasa na 903 a harkar wasansa, sama da kowane dan wasa a kasar Italiya, inda ya sha gaban Paolo Maldini.
Idan Inter Milan ta yi nasara a wasa tsakaninta da Sampdoria za ta koma saman teburin Serie A - har yanzu ba ta yi rashin nasara ba a karkashin mai horarwa Antonio Conte.