Ole Gunnar Solskjaer: 'Manchester United tana samun ci gaba'

Kocin Manchester United manager Ole Gunnar Solskjaer ya ce karamar tawagar 'yan wasan kungiyar suna samun ci gaba idan aka kwatanta da yadda suka faro kakar bana.

United ta yi nasara ne kawai a wasa daya cikin biyar da ta buga a gasar firimiyar bana.

"Ban ce wannan kakar za ta kasance mai sauki ba," in ji kocin.

"Mun samu cikas nan da can. Idan muka yi rashin nasara a wasa wajibi ne mu yarda da kanmu kuma muna yin hakan."

United wadda ta sha kashi da ci 2-0 a hannun West Ham a karshen makon jiya kuma a ranar Litinin za ta fafata da Arsenal a filin wasa na Old Trafford.

"Al'adarmu tana nan, kuma babu wata matsala da dabi'armu da aikinmu da kwazonmu," in ji shi.

"Za ku iya ganin yadda Astana da Rochdale suke so su kayarta kuma suna yin bakin kokarinsu."