Liverpool vs Sheffield: Wijnaldum ya ceci Liverpool

Liverpool ta ci gaba da zama a saman teburin Premier bayan ta sha da kyar a hannun Sheffield United da ci 1-0 a filin wasa na Bramall Lane.

An shafe minti 70 ana fafatawa ba tare da an ci wani ba kafin a minti na 70 din Georginio Wijnaldum ya ci kwallo bayan ya dada wa mai tsaron ragar Sheffield Henderson kwallo daga wajen yadi na 18.

Da wannan kwallon ne Liverpool ta dogara har karshen wasan, abin da ya sa ta ci gaba da zama a mataki na daya da makinta 21.

Har yanzu ba a doke Liverpool ba a Premier ta bana, sai dai Napoli ta doke ta a wasan gasar Zakarun Turai ta Champions League ranar 17 ga Satumba.

Ranar Laraba ne kuma za ta fafata da Red Bull Salzburg ta kasar Austria a Anfiled a Champions League, sannan ta buga wasan Premier mako na takwas da Leicester City ranar Asabar.

Wasannin Asabar: