Madrid na fargaba kan lafiyar Neymar

Nyemar

Asalin hoton, Getty Images

Har yanzu Real Madrid tana son daukar Neymar amma tana neman PSG ta ba ta tabbaci game da raunin da dan wasan yake yawan fama da shi, kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito.

Sai dai AS ta ruwaito cewa girman albashin Neymar shi ne yake kawo wa Real Madrid da Barcelona tsaiko wurin daukar dan wasan gaban mai shekara 27.

'Yan wasan Man United sun bukaci Rashford da ya rika buga finareti idan an samu bayan Pogba ya zubar da finaretin a wasansu da Wolves, a cewar rahoton Mail.

Mahaifin dan wasan bayan Arsenal Shkodran Mustafi mai shekara 27 tare da wakilinsa sun ce dan wasan yana yunkurin barin kulob din, in ji Mirror.

Manchester United na fatan sayar da Alexis Sanchez mai shekara 30 kuma dan kasar Chile kafin a rufe kasuwar saye da musayar 'yan wasan nahiyar Turai, a cewar Mirror.

Mail ta ruwaito cewa Tottenham za ta sayar da dan wasan tsakiyarta Christian Eriksen dan kasar Denmark idan ta samu tayin da ya kai akalla fan miliyan 50.

Kazalika, rahoton Football.London ya ce Tottenham din za ta iya samun damar sayen Paulo Dybala a watan Janairu idan dai har yana nan a Juventus din.

Ana sa ran Virgil van Dijk na Liverpool mai shekara 28 zai sake saka hannu kan sabuwar yarjejeniya a kulob din, abin da zai ninka albashinsa zuwa fan 250,000 a duk mako, in ji 90min.

Zinedine Zidane ba ya tsammanin mai tsaron raga Keylor Navas zai bar Real Madrid a yanzu duk da alakanta dan kasar Costa Rico din mai shekara 32 da ake yi da PSG, a cewar rahoton Marca.