Real Madrid na cinikin Neymar, United na dab da saye Llorente

Gareth Bale

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bale ya shafe shekara shida a Bernabéu

Dan wasan gaban kasar Wales Gareth Bale zai ci gaba da zama Real Madrid amma fa tilas ne ya nuna cewa "kwararren dan wasa ne", in ji koci Zinedine Zidane.

An yi tsammanin Bale mai shekara 30 zai bar Bernabéu a karshen kakar da ta gabata a yayin da Zidane ke cewa "abin zai yi wa kowa dadi", kafin daga bisani kuma Real Madrid ta dakile komarsa China da taka-leda.

Kwatsam, sai ga shi dan wasan ya bayar da mamaki a wasan farko na La Liga ta bana, wanda Real din ta casa Celta Vigo da ci 3-1.

"Sauyin da aka samu shi ne cewa dan wasan zai ci gaba da zama," Zidane ya bayyana.

A gefe guda kuma, wata tawagar jami'an Real Madrid ta sauka a Faransa domin tattauna daukar dan wasan Brazil na gaba Neymar mai shekara 27 daga Paris St-Germain in ji jaridar Marca ta Sifaniya.

Neymar na atisaye a tawagar Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ba da jimawa ba PSG ta yi watsi da tayin da Barcelona da Real Madrid suka yi a kan dan wasan

Wasu rahotanni a baya sun ce tsohuwar kungiyar Neymar, Barcelona, ta yi tayin bayar da euro miliyan 100 kari kuma da dan wasanta Philippe Coutinho wanda ya tafi Bayern Munich, domin karbar dan wasan na Brazil, amma PSG ta ki.

Haka kuma Real Madrid din na son golan Chelsea dan Argentina, Willy Caballero, mai shekara 37, kamar dai yadda jaridar ta Marca a nan ma ta ruwaito.

Ita kuwa Manchester United na dab da sayen tsohon dan wasan Tottenham kuma dan gaban Sifaniya, Fernando Llorente, mai shekara 34, kamar yadda jaridar Star ta ruwaito daga Gazzetta dello Sport.

Kazalika kungiyar ta Red Devils na fuskantar kalubalen ci gaba da biyan albashin fan miliyan 12 na Alexis Sanchez a kakar nan, ko da kuwa dan wasan gaban na Chile mai shekara 30 ya tafi zaman aro Inter Milan, kafin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta Turai a mako mai zuwa.

Sanchez bai halarci atisayen United ba a ranar Alhamis domin ya je ofishin jakadancin Amurka da ke Landan, in ji jaridar Sun.

Dan wasan tsakiya na Leicester City, dan Portuguese Adrien Silva, mai shekara 30, ya tashi zuwa Monaco ranar Juma'a domin ya je a gwada lafiyarsa. Jaridar Daily Telegraph ta ce Silva zai koma can aro ne tsawon kakar nan.

Barcelona ta yi watsi da bukatar Inter Milan ta karbar aron dan wasan tsakiya na Chila Arturo Vidal, mai shekara 32, kamar yadda Mundo Deportivo ta labarto.

Shi kuwa dan wasan gefe na Chelsea kuma dan Brazil Kenedy, mai shekara 23, yana duba yuwuwar barin kungiyar dindindin kafin a rufe kasuwar sayar da 'yan wasa ta Turai da ke ci yanzu.

Kungiyar Fenerbahce ta nesanta kanta da maganar sayen dan wasan baya na Manchester United kuma dan Argentina Marcos Rojo, mai shekara 29, in ji Star.