Coutinho ya koma Bayern Munich daga Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta dauki Philippe Coutinho daga Barcelona a matsayin aro na shekara daya tare da damar sayensa gaba daya nan gaba.
Barcelona ta ce zakarun na Jamus za su biya fam miliyan 7.78 domin daukar dan wasan na Brazil, mai shekara 27, sannan za su iya sayensa a kan fam miliyan 109.84.
Bayern za kuma su biya albashin Coutinho na tsawon lokacin da zai shafe a Jamus.
"Wannan sauyi wata dama ce ta fuskantar sabon kalubale a wata kasa ta daban da kuma daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai," a cewarsa.
"Ina matukar farin ciki da hakan. Kuma ina da manufofin da nake son cimmawa kamar yadda Bayern ita ma take da su. "
Coutinho ya koma Barcelona ne daga Liverpool kan fam miliyan 142 a watan Janairun 2018.
Duk da cewa ya zura kwallo 21 a wasa 76 a Sifaniya, ya gaza cimma burin da aka dora masa tun farko, abin da ya sa aka rinka alakanta shi da komawa wasu kungiyoyin ciki har da Liverpool da Arsenal da kum Tottenham.







