Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa PSG ta ajiye Neymar a karo na biyu?
A karo na biyu sunan Neymar bai fito a jerin sunayen 'yan wasan da za su buga wa kulob din Paris St-Germain ba.
Dan wasan mai shekara 27 wanda bai buga wa PSG wasan farko ba wanda ta yi da Nimes a karshen makon da ya gabata, ya zama dan wasan da Barcelona da Real Madrid ke zawarci.
To sai dai har yanzu PSG ba ta daidaita da kowane kulob ba kan dan wasan.
Koci Thomas Tuchel ya ce "ba zai kasance tare da mu ba" a wasan ranar Lahadi a Rennes, inda ya kara da cewa har yanzu bai warware ba saboda haka ba zai iya buga wasa ba.
Tuchel ya ce har yanzu babu wani dan wasan gaba kamar Neymar a kulob din nasa duk da ya amince da cewa ba a san makomar Neymar a PSG ba.
"Idan na yi tunanin 'yan wasan da za su karfafa PSG, ina kawo Neymar a ciki", In ji Tuchel.
Neymar, wanda ya zama dan kwallon da ya fi kowanne tsada a 2017, lokacin da ya koma PSG daga Barcelona a kan euro miliyan 222 , ya ci kwallaye 34 a kakar wasa guda biyu a Parc des Princes.
A wasan da PSG ta ci Nimes 3-0, 'yan kallo sun ta daga kyallaye da ke nuna sun gaji da Neymar da 'ya wuce ya ba su wuri', bayan da darektan wasanni Leonardo ya bunta cewa ana samun nasara dangane da tattaunawar barin Neymar kulob din.