Barca da PSG sun gana kan Neymar, Ina Sanchez zai koma?

Jami'an Paris St-Germain da Barcelona sun gana a karon farko domin tattaunawa kan makomar Neymar, mai shekara 27, sai dai ba wata yarjejeniya da suka cimma a tattaunawar ta tsawon sa'a uku. (Le Parisien)

Barcalona ta ce a shirye ta ke ta biya fam miliyan £93m hadi da dan wasan Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27, da kuma dan wasan Croatia Ivan Rakitic, mai shekara 31 duk a madadin Neymar. (ESPN)

Barcelona na son karbar aron Neymar domin ya dawo Nou Camp a wannan kasuwar musayar 'yan wasa kafin tabbatar da cinikinsa daga PSG. (Independent)

Manchester United ba za ta saurari duk wata bukata ba kan dan wasan tsakiyarta Paul Pogba, mai shekara 26, kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa a Turai. (Telegraph)

Manchester United za ta biya Alexis Sanchez kudaden albashi idan har dan wasan na Chile mai shekara 30 ya amince ya koma Roma. (Sun)

Dan wasan baya na Croatia Dejan Lovren, ,mai shekara 30, ya kauracewa atisayen Liverpool a yayin da take shirin karawa da Chelsea a wasan Super Cup bayan ta fara tattaunawa da Roma. (Mirror)

Kungiyar Brazil ta Flamengo ta tafi Faransa domin tattaunawa da Marseille kan dan wasan na Italiya Mario Balotelli, mai shekara 29, (Corriere dello Sport)

DC United ta taya tsohon dan wasan Ingila Daniel Sturridge, mai shekara 29, wanda ya bar Liverpool a kakar da ta gabata. (ESPN)