Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier: Man City da Tottenham da Liverpool sun fara da kafar dama
Manchester City ta fara farautar lashe kofin Premier karo uku a jere bayan ta caccasa West Ham a ranar farko na soma gasar a bana.
Na'urar VAR da aka fara amfani da ita a karon farko a gasar Premier, ta taka rawa sosai ga nasarar da City ta samu inda lallasa West Ham ci 5-0.
Kwallaye uku rigis Raheem Sterling ya jefa, yayin da Gabriel Jesus da Sergio Aguero, suka ci sauran kwallayen a bugun fanariti.
Harry Kane kwallaye biyu ya ci wanda ya taimaka Tottenham doke Aston Villa ci 3-1. Aston Villa ce ta cin Tottenham ta kafar John McGinn, kafin daga bisani Tanguy Ndombele, ya farke wa Tottenham.
Ana saura minti hudu a hure wasan, Kane ya zira kwallaye biyu.
Sheffield United, da ta hauro gasar Premier a bana bayan shekara 12 ta yi 1-1 ne da Bournemouth. Haka ma Everton, ta tashi babu ci tsakaninta da Crystal Palace.
Brighton, da ta sha da kyar a Premier a bara ta fara da kafar dama a bana inda ta casa Watford 3-0. Haka ma Burnley ta doke Southampton, ci 3-0.
Wasanni uku za a buga ranar Lahadi, ciki har da gwabzawa tsakanin Manchester United da Chelsea a Old Trafford.
Karon farko kenan da Frank Lampard zai jagoranci Chelsea a gasar Premier.