Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pogba ya kosa ya koma Madrid, Juve na zawarcin Sanchez
Dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 26, ya kagara ya bar Manchester United don koma wa Real Madrid, in ji Marca.
Dan wasan Ingila Harry Maguire, mai shekara 26, ya ki karbar tayin fan 278,000 a mako don ya koma Manchester City maimakon abokiyar hamayyarta United, kamar yadda kafar yada labarai ta Star ta bayyana.
Kocin United din Ole Gunnar Solskjaer yana tattaunawa da dan wasan Tottenham Christian Eriksen dangane da yiwuwar komawarsa kungiyar, a cewar Manchester Evening News.
Hakazalika dan wasan Man Utd Alexis Sanchez, mai shekara 30, ya shirya koma wa Italiya, inda Juventus da Napoli da AC Milan da kuma Inter Milan duka suke zawarcin dan kwallon, kamar yadda jaridar Mirror ta ruwaito.
Sanchez zai ci gaba da yunkurin barin United gabanin rufe kasuwar saye da musayar 'yan wasan nahiyar Turai a ranar 2 ga watan Satumba, in ji Times.
Juventus tana ci gaba da shirye-shiryen rabuwa da Paulo Dybala, mai shekara 25, gabanin rufe kasuwar - duk da cewa har yanzu ba ta samu tayi mai tsoka ba daga wata kungiyar, a cewar jaridar Independent.
Daraktan wasanni na Paris St-Germain Leonardo ya ce dan wasan Brazil Neymar "ya yi kura-kurai" amma duk da haka dan wasan zai ci gaba da zama a birnin Paris "har shekara uku", in ji RMC.
Akwai yiwuwar dan wasan Argentina Marcos Rojo, mai shekara 29, wanda Everton ke zawarci, zai iya barin Man Utd kafin rufe kasuwar saye da musayar 'yan wasan nahiyar Turai, a cewar Express.
Dan wasan Liverpool da kuma Croatia, Dejan Lovren, mai shekara 30, yana gab da kammala kulla yarjejeniya da AS Roma a kan fan miliyan 23, in ji (Calcio Mercato ta hannun Mirror).