Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lionel Messi ya kere Cristiano Ronaldo a daukar albashi
Dan wasan Barcelona kuma dan kasar Argentina Lionel Messi ya zama dan wasan da ya fi kowa daukar albashi a duniya.
Mujallar Forbes wacce ta wallafa rahoton karin yawan albashin 'yan wasa 100, ta ce Messi yana daukar dala miliyan 127 a shekara,
Abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo na Juventus Cristiano Ronaldo ne ke matsayi na biyu, wanda yake daukar dala Miliyan 109.
Neymar na PSG ne na uku wanda yake karbar dala Miliyan 105.
Serena Williams ce kawai mace a cikin jerin sunayen 'yan wasa 100 da ke daukar dala miliyan 29.
A bara Floyd Mayweather ne ya fi kowa daukar albashi amma yanzu Messi ya karbe matsayin.
Rahoton kuma ya bayyana cewa Amurka ce ta fi yawan 'yan wasan da suka fi daukar albashi, inda take da 'yan wasa 62 cikin 100, sai Birtaniya da ke matsayi na biyu da yawan 'yan wasa biyar, sai kuma Faransa da Spain da ke da uku-uku.
Dan wasan Manchester United Paul Pogba ne ya fi karbar kudi a gasar Premier, inda yake matsayi na 44 da fam miliyan £25.9m da yake karba a shekara.
'Yan wasa 10 na farko
1. Lionel Messi $127m (£99.8m)
2. Cristiano Ronaldo $109m (£85.6m)
3. Neymar $105m (£82.5m)
4. Canelo Alvarez $94m (£73.8m)
5. Roger Federer $93.4m (£73.3)
6. Russell Wilson $89.5m (£70.3m)
7. Aaron Rodgers $89.3m £70.1m)
8. LeBron James $89m (£69.9m)
9. Stephen Curry $79.8m (£62.7m)
10, Kevin Durant $65.4m (£51.3m)