Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Neymar 'ba ya son' komawa Madrid, City na 'neman' Joao Cancelo
Dan kwallon Brazil Neymar, mai shekara 27, ya yi watsi da tayin koma wa Real Madrid inda ya shaida wa kungiyarsa ta PSG cewa Barcelona yake muradin komawa, a cewar jaridar Express.
Dan wasan kungiyar Juventus da kasar Portugal Joao Cancelo, mai shekara 25, yana kan hanyarsa ta koma kungiyar Manchester City a kan kudi fam miliyan 44, in ji kafar yada labarai ta Goal.
An yi wa Tottenham tayin sayen dan wasan Jamus Julian Draxler, mai shekara 25, don ya maye gurbin dan wasan Denmark Christian Eriksen, mai shekara 27, wanda zai bar kungiyar, kamar yadda jaridar Star ta ruwaito.
Everton ta shaida wa Tottenham cewa tana son dan kwallon Ingila, Danny Rose, mai shekara 28, in ji Star.
Manchester United tana zawarcin dan wasan Ajax, Matthijs de Ligt, sai dai dan kwallon yana son ya koma PSG ne, ko kuma Barcelona, in ji Marca.
Kodayake kafar yada labarai ta ESPN ta ce ana kyautata zaton cewa PSG ce za ta sayi dan kwallon.
Manchester United tana kokarin sayen manyan 'yan wasa biyu kafin fara wasannin tunkarar kaka mai zuwa, a cewar jaridar Sun.
United tana neman dan wasan Monaco, Youri Tielemans, mai shekara 22, wanda yake kungiyar Leicester City a matsayin aro, idan Paul Pogba ya bar kungiyar a kakar bana, in ji jaridar Independent.
Karanta wasu karin labarai