Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea za ta 'sayar' da Hazard a kan €100m, PSG na neman De Gea
Chelsea ta ce Real Madrid ta biya ta Yuro miliyan 100 don mallakar dan wasan Belgium Eden Hazard, in ji jaridar Guardian.
Paris St-Germain tana neman golan Manchester United David de Gea, mai shekara 28, don ya maye gurbin golan Italiya, Gianluigi Buffon, mai shekara 41, a cewar (Times - subscription required).
Dan wasan Liverpool da kuma Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 27, yana son ya sabunta yarjejeniyarsa a Anfield, in ji ESPN.
Manchester United ta ce a shirye take ta yi watsi da duk wani tayi da za a yi wa dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 26, in ji jaridar Mail.
Hakazalika nan gaba kadan ne United din za ta sanar da sayen dan wasan Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 24, a matsayin dan wasan da za ta saya na farko a kakar bana, in ji jaridar Star.
Borussia Dortmund tana fatan dan wasan Jamus Mario Gotze, mai shekara 27, zai sanya hannu a sabuwar yarjeniyar bayan an ruwaito cewa Arsenal tana zawarcinsa, in ji (Bild, in German).