Jose Mourinho: Manchester United ba za ta koma wa kamar Da ba

Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manchester United ta tsallake zagaye na gaba a zakarun turai bayan ta doke Young Boys 1-0

Jose Mourinho ya amsa cewa akwai bukatar gyara a Manchester United, amma yana ganin ba adalci ba ne a kwatanta su da martabar kungiyar a shekarun baya.

United da ke matsayi na bakwai a teburin Firimiya za ta ziyarci Southampton a ranar Asabar, kuma tazarar maki 14 tsakaninta da Manchester City.

Mourinho ya ce wasa ya canja a yanzu, don haka yana da wahala a iya maimaita abin da ya faru a baya.

"Yanzu akwai wahalar sayen manyan 'yan wasa," in ji Mourinho.

"A shekarun baya, kananan kulub har rokon manyan kulub suke yi su saye zaratan 'yan wasannsu suna son sayarwa."

"Na sani dole akwai bukatar gyara, amma abu daya shi ne mu kara kwazo. Kwatanta kanmu da matsayin Manchester United a baya abu ne mai wahala," in ji Mourinho.

Ya ce ko Manchester United yanzu tana son 'yan wasan Tottenham Harry Kane da Dele Alli, ba za ta iya sayensu ba, sabanin yadda zamanin Sir Alex Ferguson ya karbo Michael Carrick kan fam miliyan 18 domin maye gurbin Roy Keane.

Mourinho ya ce "duk da Tottenham babban kulub ne amma kowa ya san Manchester United ta sha gabanta, a tarihi da girma, amma ko za ka iya sayen manyan 'yan wasan Tottenham? amsar ita ce aa"

Ya ce kwallo ta sauya a yanzu. " Shin Manchester United na iya sayen Harry Kane da Dele Alli da Eriksen da Son? aa. don haka wane ne babba? Manchester ko Tottenham?"

A cewar Mourinho, "yanzu idan kana bukatar babban dan wasan sai ka ware makudan kudi, kuma ko matsakaicin dan wasa kake nema sai ka ware manyan kudi, don haka na yarda da abin da mutane ke cewa Manchester yanzu ba ta Da ba ce."