Najeriya ta ayyana dokar ta-baci kan ambaliyar ruwa

Ambaliyar ta fi kamari ne a jihohi hudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ambaliyar ta fi kamari ne a jihohi hudu ciki har da Kogi inda aka dauki wannan hoton

Gwamnatin Najeriya ta yi shelar yanayin ta-baci a jihohi hudu na kasar sanadiyyar ambaliyar ruwa da ke ci gaba da barna.

Jihohin sun hada da Neja da Kogi da Delta da kuma Anambra, yayin da za a ci gaba da nazarin yanayin da ake ciki a wasu jihohi da ambaliyar ta shafa.

Mutane fiye da dari ne dai ambaliyar ta kashe cikin kimanin makwanni biyu a cewar Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya wato NEMA.

Injiniya Mustapha Yunusa Maihaja shi ne shugaban hukumar ta NEMA, wanda kuma ya yi shelar yanayin ta-bacin, a madadin shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Ya kuma yi wa Ishaq Khalid na BBC karin bayanin cewa shelar na nufin amfani da dukkan kayan aiki da ma'aikata da suka dace wajen tunkarar bala'in.

flood in nigeria

Manoma da kuma wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su na ci gaba da kokawa a Najeriya dangane da irin barnar da matsalar ta haifar a daminar bana.

An dai tafka gagarumar asara a sassa daban-daban na kasar dalilin ambaliyar.

Mutane fiye da dari ne dai ambaliyar ta kashe cikin kimanin makwanni biyu a cewar Hukumar Agajin gaggawa ta kasar wato NEMA.

Mutanen da lamarin ya rutsa da su dai suna kaurace wa ambaliyar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutanen da lamarin ya rutsa da su dai suna kaurace wa ambaliyar