An kashe Abzinawa 40 a Mali

Rahotanni daga Mali sun ce wasu da ake zargi mayaka masu ikirarin jihadi ne sun kashe Abzinawa fiye da 40 a wasu hare-hare biyu da aka kai arewa maso gabashin kasar.

Shugabannin Abzinawan sun ce lamarin ya faru ne a ranakun Alhamis da Juma'a a kusa da iyakar Nijar.

Mazauna yankin na cewa Abzinawa na fuskantar hare-hare ne sakamakon harin da suka kai wa sansanonin masu da'awar jihadin a kwana nan.

Jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, sun bayyana samun sahihan rahotanin da ke cewa mayakan Abzinawa sun kashe akalla mutum 95 a farmakin fatatakar masu ikirarin jihadi da suka kaddamar makonni biyu da suka gabata.

Arewa maso gabashin Mali na fama da rashin doka da oda duk da cewa akwai dakarun wanzar da zaman lafiya a yakin, da kuma yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Abzinawan a shekara ta 2015.

Abzinawa, wadanda asalinsu makiyaya ne sun kwace yankuna da dama a kasar, ciki har da garin Timbuktu mai matukar tarihi, a shekarar 2012.

Sai dai daga baya, mayaka masu da'awar jihadi da ke da alaka da al-Qaeda sun kwace yankin, da cire tutar dakarun da Faransa ke jagoranci a 2013.

Daga shekara ta 1960 bayan samun 'yanci da Mali ta yi daga Faransa sau 4 kasar na fuskantar tawaye.