Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane a Mali
Hukumomi a kasar Mali sun ce mayakan da ke da'awar jihadi a kasar sun kai wani hari da ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutum hudu a yankin arewacin kasar.
Mayakan sun kai harin ne a garin Talataye a ranar juma'a, kuma rahotanni sun ce mayakan sun yi awon gaba da mutane da dama.
Harin na zuwa ne bayan da rundunar sojin Mali ta haramta zirga-zirgar babura da kuma mota a kori-kura, da mafi yawanci mayakan ke amfani da su.
A Kalla mutum 50 suka mutu a wasu hare-hare biyu da 'yan kungiyar suka kai a yankin a watan da ya gabata.
An dai samu sassaucin hare hare bayan shigar sojojin Faransa domin wanzar da tsaro amma har yanzu ana fuskantar barazanar a arewacin Mali.