Yadda Mo Salah ya yi kaca-kaca da AS Roma

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta doke AS Roma da ci 5-2 a wasan farko na wasan daf da na kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.
Liverpool, wacce ta mamaye mafi yawancin wasan wanda aka yi a Anfield, ta zura kwallayen biyun farko ta hannun Mo Salah kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Bayan an dawo ne kuma Sadio Mane ya ci ya uku, kafin Famino ya zura ya hudu da ta biyar.
Ana daf da tashi ne Roma ya bude wuta inda ya zura kwallaye biyu cikin kankanin lokaci.
Hakan dai ya sa sun samu kwarin gwuiwa a wasan na biyu da za su fafata musamman ganin yadda suka yi wa Barcelona a zagayen da ya gabata.
Mohamed Salah ya zura kwallo 43 a dukkan wasannin da ya buga a kakar bana.
Yayin da ya ci 10 a gasar ta zakarun Turai - Cristiano Ronaldo ne kawai ya fi shi zura kwallo a gasar a bana.
A ranar Laraba ne Bayern Munich za ta karbi bakuncin Real Madrid a daya wasan na fab a na karshe.











