Xavi zai yi ritaya a karshen kakar wasan bana

Tsohon dan wasan Barcelona Xavi ya shirya domin ya yi ritaya a karshen kakar wasa ta bana, ya kuma fara aikin koci.

A yanzu haka dai dan shekara 37 din, wanda ya lashe gasar zakarun Turai sau hudu da gasar cin kofin duniya, yana murza leda ne wa kungiyar kwallon kafa ta Qatar Al-Sadd.

Amman yana jin iya mayar da kuzarinsa bayan wasa yana raguwa.

Ya ce: "Lallai wannan zai kasance shekarata ta karshe a taka tamaula. Ina son in samu lasisina na zama koci a shekara mai zuwa."

Xavi, wanda ya buga wa Spaniya kwallo sau 133 a shekara 14 da yayi yana murza mata leda kuma ya samu ya ci gasar kofin duniya a shekarar 2010, ya ce lokacin da ya yi a Gabas ta tsakiya ta ba shi damar hutawa.

Karanta wasu labaran: