Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An tsayar da ranar karawa tsakanin Real da Barca
Hukumar kwallon kafar Spaniya ta tsayar da lokacin da za a kara tsakanin Real Madrid da Barcelona a wasan La Ligar karawar mako na 23 a Santiago Bernabeu.
Hukumar ta amince kungiyoyin biyu da ke hamayya da juna su kara a ranar Asabar 23 ga watan Disambar 2017 da karfe 12 agogon Nigeria da Niger.
A ranar Asabar 4 ga watan Satumba za a ci gaba da wasannin mako na 11, inda Barcelona za ta karbi bakuncin Sevilla, ita kuwa Real Madrid za ta kece raini ne da Las Palmas.
Bayan da aka buga wasannin mako na 10 a gasar bana, Barcelona tana ta daya a kan teburi ta kuma bai wa Real Madrid wacce take ta uku tazarar maki takwas.