Super Eagles na gab da zuwa Russia 2018

Yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, Najeriya ce a kan gaba a rukunin B da maki 10

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya suna gab da samun tikitin zuwa wasan cin kofin duniya wanda za a yi a badi a kasar Rasha.

A ranar Asabar ne Najeriya za ta kara da Zambia a filin wasa na Godswill Akpabio da ke jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya.

Idan Najeriya ta samu nasara a wasan, hakan yana nufin ke nan ta samu tikitin zuwa kasar cin kofin duniya wanda za a yi a shekarar 2018.

A karawar kasashen ta farko wanda kasar Zambia ta karbi bakunci, Najeriya ce ta samu nasara da ci 2-1.

Karanta wadansu karin labarai masu kayatarwa