Nigeria: Chatin ya maye gurbin kiran waya

Matasa a Najeriya sun fi yin catin maimakon kiran waya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matasa a Najeriya sun fi yin chatin maimakon kiran waya

Yanzu jama'a da dama a Najeriya sun fi mayar da hankali wajen amfani da kafafan sada zumunta da muhawara domin tattaunawa da ake cewa chatin, maimakon kiran waya.

Bincike ya nuna cewa matasa su ne suka fi chatin din a kan manya.

Wasu matasa da BBC ta tattauna da su sun ce, sun fi jin dadin chatin din, maimakon kiran wayar, saboda ko ba komai za a jima ana hira ba kamar kiran waya ba.

Yayin da wasu matasan suka ce, suna chatin ne domin nishadi, kuma ta hanyar amfani da kafafan sada zumuntar ana iya aika hotuna da ma bidiyo, ba kamar kira ba.

Wasu masu lura da harkokin sadarwa a Najeriyar sun ce, suna ganin yanzu an fi karkata ne ga chatin a maimakon kiran waya saboda kiran na jan kudi sosai.

Hakan ya sa yawancin matasan sukan gwammace su sayi data su yi chatin, maimakon su saka kati su kira waya.

Ana dai amfani da hanyoyin sadarwa da suka hada da Whatsapp da Facebook da Twitter da Instagram da dai sauransu wajen yin chatin.