Madrid za ta sayi Mbappe mafi tsada a duniya

Real Madrid ta shirya sayen Kylian Mbappe kan kudi Yuro miliyan 180 daga Monaco a bana in ji jaridar Marca.

A labarin da ta wallafa ta ce wannan kudin da Madrid za ta biya Monaco zai haura wanda Manchester United ta sayi Paul Pogba daga Juventus a 2016.

Madrid din za ta fara biyan Monaco Yuro miliyan 160 daga baya ta karasa biyan Yuro miliyan 20 da sauran tsarabe-tsaraben da zai saka hannu kan yarjejeniya.

Jaridar ta ce da PSG ta dauki Neymar kan Yuro miliyan 222 daga Barcelona wanda ya ce zai ci gaba da zama a Nou Camp, da shi ne zai zama mafi tsada a banar.

Wannan kuma ba shi ne karon farko da Real Madrid ke sayan 'yan kwallo mafi tsada a duniya ba.