Southampton ta fitar da Arsenal a League Cup

Asalin hoton, Getty
Kulob din Southampton ya doke Arsenal da ci 2-1, kuma ya yi waje da kungiyar a gasar League Cup da suka kara a Emirates ranar Talata.
Arsenal ce ta fara zura kwallo a ragar Southampton ta hannun dan kwallonta Alexis Sanchez ta hanyar bugun tazara.
Nan ta ke Southampton ta farke kwallonta a bugun Fenariti da Dusan ya buga ya kuma ci a ketar da aka yiwa Sadio Mane.
Southampton karkashin koci Ronald Koeman ta kara kwallo ta biyu a raga ta hannun Nathaniel Clyne saura mintuna biyar a tafi hutun rabin lokaci.
Sauran sakamakon wasannin da aka kara:
Cardiff 0 - 3 Bournemouth Derby 2 - 0 Reading Leyton Orient 0 - 1 Sheff Utd Liverpool 2 - 1 Middlesbrough MK Dons 2 - 0 Bradford Shrewsbury 1 - 0 Norwich Sunderland 1 - 2 Stoke Swansea 3 - 0 Everton Fulham 2 - 1 Doncaster







