Ancelotti ya bukaci Madrid ta kara kaimi

Asalin hoton, AFP
Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bukaci 'yan wasa su kara zage damtse a wasa, duk da doke Deportivo La Coruna 8-2 da suka yi a gasar La Liga ranar Asabar.
Cristaino Ronaldo ne ya zura kwallaye uku rigis a raga, kuma jumulla yana da kwallaye bakwai kenan a gasar La Liga.
Sauran 'yan wasan da suka zura wa Madrid kwallaye sun hada da Rodríguez sai Bale da kuma Hernández da kowannensu ya zura kwallaye biyu a raga.
Ancelotti ya ce "Ya kamata 'yan wasa su kara kaimi, domin suna da fitattu kuma kwararrun 'yan kwallon da za su fitar da kungiyar kunya".
Bayan da aka doke Madrid a wasanni biyu a gasar cin kofin La Ligar Spaniya, sai dai kuma ta zura kwallaye 13 a raga a gasar.







