Debuchy zai yi jinyar makonni shida

Asalin hoton, AFP
Dan kwallon Arsenal, Mathieu Debuchy zai yi jinyar makonni shida sakamakon rauni a idon sawunsa abinda zai tilasta a yi masa tiyata.
Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce dan wasan mai shekaru 28 ya ji rauni ne a wasansu da Manchester City a ranar Asabar.
Wenger kuma ya yi watsi da sukar da ake yi wa Mesut Ozil wanda ake cewar bai taka rawar gani ba a wasansu na tsakiyar mako tsakaninsu da Borussia Dortmund.
Kocin ya bukaci magoya baya su marawa Ozil baya domin samun nasarar kulob din.
Arsenal za ta buga wasa da Aston Villa a ranar Asabar inda ake saran Calum Chambers zai maye gurbin Debuchy.







