Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Shin ko mace na gadon kurajen fuska?
Latsa hoton sama domin sauraren shirin
Kungiyar kwararrun likitocin fata ta Amurka da Canada wato AAD ta ce ana samun wasu mutanen da ke kurajen fuska da girmansu.
Inda ta ce cutar na kama wasu a lokacin da suke da shekara 30 da doriya ko 40 da doriya ko ma shekara 50 da wani abun.
Kungiyar ta kara da cewa ga masu shekaru hamsin da ke kurajen, an fi samun hakan a tsakanin matan da ke cikin shekarun daina jinin al'ada.
Haka kuma masu binkice sun gano cewa wasu mutane na gadon kurajen fuska, musamman wadanda ke samun kurajen a lokacin da suka girma.
Sai dai mata sun fi maza samun kurajen fuska a shekaru 30 zuwa hamsin, a cewar ta.
Kungiyar ta bayyana wasu dalilai da ta ce su ne suke janyo kurajen fuska a wadannan shekaru.
Wadanda suka hada da rashin daidaito a kwayoyin halitta na hormones.
Da shan wasu magungunan asibiti.