Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Mace mai ƙugun maza kan gamu da tangarda a wajen haihuwa
Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa, samun tangarda a yayin nakuda na daga cikin muhimman dalilan da ke janyo mutuwar mata masu juna biyu a fadin duniya.Ire-iren tangardar da mata kan fuskanta kan zamanto a wasu lokuta yana da alaka da irin halittar kugunsu. Haka kuma mata masu karamin kugu ka iya fuskantar tangarda domin kan ɗa zai yi wahalar fita.
Likitoci sun ce siffar halittar kugu kala hudu ce, sai dai guda daya ne ya fi dacewa da haihuwa ba tare da wata matsala ba. Kuma yawancin mata na da wannan halittar kugun da jariri zai ratsa ya fitoba tare da an samu tangarda ba.Masana sun tabbatar da cewa samun tangarda a lokacin nakuda kan sa nakudar ta yi tsawo, kuma hakan na iya jefa rayuwar uwa da jaririnta cikin hatsari.Lamarin da ke janyo asarar rayukan mata masu juna biyu, musamman a nahiyar Afrika.Nahiyar da ke da karancin kwararrun ma'aikatan lafiya, idan aka kwatanta da yawan al'ummarta. Hukumar lafiya ta duniya ta ce akalla mata masu juna biyu kusan dubu 300 ne suka mutu a shekarar 2017. Kashi daya bisa uku na wannan adadi, a cewarta sun mutu ne a kasashen Najeriya da Indiya.