Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Ana warkewa daga cutar taɓin hankali?
Latsa hoton da ke sama da sauraron hirar da Fauziyya Kabir Tukur ta yi da Dokta Ɗayyiba Shaibu
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce cutar gushewar hankali ko ciwon hauka matsala ce mai wahala da ke shafar aƙalla mutum miliyan 20 a faɗin duniya.
Cutar gushewar hankali cuta ce ta ƙwaƙwalwa da kan iya janyo gane-gane da jin muryoyin mutanen da ba sa nan da sa wa rai wani abu da ba shi ne ba da tsoro na babu gaira babu dalili.
Alamomin cutar gushewar hankali
- Rikirkitaccen tunani
- Tsananin damuwa
- Amfani da kalaman da ba a saba ba
- Tsananin sauyi a halayya
- Gane-gane da jin muryoyin da babu
- Hasashen abin da ba haka ba ne
- Rashin yarda da 'yan uwa ko makusanta
Me ke janyo cutar gushewar hankali?
WHO ta ce har yanzu bincike bai gano taƙamaimai abin da ke janyo cutar gushewar hankali ba.
Amma ana tunanin cewa ana gadonta kuma halittar mutum da al'amuran da ke faruwa a rayuwarsa na yau da kullum na haifar da cutar.
WHO ta ce akwai yiwuwar mutanen da ke fama da cutar gushewar hankali za su riga masu lafiya mutuwa.
Wannan na da nasaba da cutukan zuciya da rashin wadataccen abinci da sauran cutuka da kan kama sassan jiki.
Masu fama da wannan matsala na fuskantar tsangwama da kyara da wulaƙanci wanda a lokuta da dama hakan kan ƙara jefa su cikin mawuyacin hali.
Amma hukumar ta ce ana warkewa daga hauka idan aka je asibiti.
Akwai taimako na musamman da ake ba su kamar magunguna da ɗebe kewa da shawarwari da ke taimaka wa wajen samun lafiyarsu.