Lafiya Zinariya: Taɓin hankalin da ke samun mutum bayan shiga tashin hankali

Latsa hoton da ke sama don saurarar hirar da Fauziyya Kabir Tukur ta yi da likita.

Sau da yawa, bayan fuskantar tashin hankali kamar hatsari ko gobara ko 'yan fashi ko yaƙi mutum kan shiga wani irin yanayi na firgici da fargaba.

Likitoci sun ce wannan wani nai'i ne ana taɓin hankali wanda a turance a ke cewa Post Traumatic Stress Disorder ko PTSD.

Sai dai ƙwararriya a ɓangaren lafiyar ƙwaƙwalwa Dokta Dayyiba Shaibu ta asibitin The Oleaster da ke Abuja a Najeriya ta ce sai an yi a ƙalla wata guda da fuskantar tashin hankali kafin a ce mutum na da cutar.

"Ba wai daga faruwar lamarin ake ganin alamomin cutar PTSD ba. Wani ma sai bayan watanni sannan alamomin za su bayyana a tattarre da shi," a cewarta.

Alamomin cutar PTSD

Dokta Dayyiba ta ce manyan lamaonin cutar sun haɗa da:

  • Yawan firgici
  • Waige-waige
  • Fargaba
  • Rashin bacci ko katsewar bacci a farka cikin firgici
  • Mutum ya riƙa tuna mummunan lamarin da ya faru da shi
  • Sauti da ƙamshi kan tuna wa mutum lamarin da ya faru (misali kukan jariri ko na ƙananan yara kan tuna wa mahaifi ko mahaifiyar da ɗansu ko ƴarsu da mota ta bankaɗe ko kuma ƙara mai ƙarfi ta tuna wa sojan da ya je fagen yaƙi da ƙarar bindiga ko bam)
  • Munanan mafarkai musamman na tashin hankalin da aka fuskanta wanda mutum zai ji kamar da gaske abin na faruwa a lokacin.

Dokta Ɗayyiba ta ce idan mutum ya fuskanci wani tashin hankali, bai kamata a riƙa yawan yi masa maganar lamarin ba.

Ta ce wannan zai zama kamar ana masa famin ciwon da ke ransa ne.

Abin da ya fi dacewa shi ne a nemar masa taimakon ƙwararru a asibitin masu fama da taɓin hankali.

"Wannan cuta ce da dole sai an nemi maganinta, saboda wannan firgici ba ya taɓa rabuwa da mutum idan ba a magance shi ba.

"Sau da yawa mun fi bayar da shawrwari da ɗebe wa marar lafiyar kewa. Ba lallai sai ya sha magunguna ba ma," a cewar Dokta Ɗayyiba.

Haka kuma, likitar ta ce ba sai mutum ya nuna alamomin wannan cuta sannan za a kai shi asibiti ba.

"In dai mutum ya shiga ko ya fuskanci wani tashin hankali, ko bai fara nuna alamomin PTSD ba ya kamata a nemi taimakon ƙwararru tun wuri," in ji ta.

Ta ce tunda shi ma nau'i ne na taɓin hankali kuma kowa da irin halittarsa wani ba shi da juriyar fuskantar mummunan tashin hankali ba tare da ya shafi lafiyar ƙwaƙwalwarsa ba.

Shi ya sa zuwa asibiti ke da amfani, a cewarta.