Juve na son Beto, Ina Bruno Fernandes zai tafi?

Lokacin karatu: Minti 1

Nottingham Forest ta taya ɗanwasan gaba na Crystal Palace Jean-Philippe Mateta kan fam miliyan 35, amma Eagles na son fam miliyan 40 kuma ba za ta bar ɗanwasan na Faransa tafiya ba har sai an lale mata kuɗin. (Athletic - subscription required)

Ɗanwasan gaba na Everton da Guinea-Bissau Beto, mai shekara 27, na cikin zaɓin da Juventus ke da shi yayin da take lalaben ɗanwasan gaba kafin rufe kasuwar cinikin ƴanwasa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Juventus kuma na son ɗanwasan gaba na Liverpool da Italiya Federico Chiesa, mai shekara 28, da kuma ɗanwasan gaba Joshua Zirkzee, da ke taka leda a Manchester United. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Ɗanwasan gaba na Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 27 na Paris St-Germain da ke murza leda a matsayin aro a Tottenham wani zaɓi ne da Juventus take dibawa. (Fabrizio Romano)

Ɗanwasan tsakiya na Manchester United Bruno Fernandes zai jira sai ƙarshen kaka kafin tabbatar da makomarsa inda kwangilar ɗanwasan za ta kawo ƙarshe a 2027 duk da yana da zaɓin ƙarin shekara guda. (Mirror).

Atletico Madrid na tattaunawa da Atalanta domin karɓo ɗanwasan tsakiya na Brazil Ederson. (AS - in Spanish)

Everton ta yi watsi da tayin Lazio kan ɗanwasan tsakiya na Ingila Tim Iroegbunam. (Corriere dello Sport - in Italian)

Wolves ta yi watsi da tayin fam miliyan 6.9 daga Roma kan ɗanwasanta na baya David Moller Wolfe. (Sky Sports)

Tsohon kocin Southampton da Rangers Russell Martin na cikin waɗanda ake tunanin Leicester City za ta ɗauko bayan bayan korar Marti Cifuentes. (Football Insider)