Sauyin yanayi: Ta yaya za mu gane idan matsanancin zafi da fari da guguwa na faruwa ne saboda ɗumamar duniya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Nidale Abou Mrad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Wasu ɓangarori na Pakistan da Indiya sun fuskanci yanayin zafi matsananci da ya kai 50C a 'yan makwannin nan. Habasha da Somalia na ci gaba da fuskantar fari mafi tsanani a tsawon shekaru. A Iraƙi kuma, wani jerin guguwa da aka dinga yi sun sa an kwantar da mutane da dama a asibiti tun daga watan Afrilu.
"Kun ga abin da sauyin yanayi ke yi ga duniya," a cewar masu amfani da shafukan zumunta. Amma shin abu ne mai yiwuwa a iya gano cewa waɗannan yanaye-yanayen da muke fuskanta na da alaƙa da sauyin yanayi da kuma ɗumamar duniya?
Alhakin yanayi
Gajeriyar amsa ita ce eh. An samu haɗin kai tsakanin ƙwararru a kan kimiyya cewa za su iya amsa tambaya kan yadda sauyin yanayi ke shafar wani abu da ke faruwa sakamakon wani sashen ilimi da suke kira Extreme Event Attribution.
Wani sabon fagen ilimi ne na kimiyya, a cewar Dr Thomas Smith, wani mai shirin zama farfesa a sashen kimiyyar muhalli a Makarantar Tattalin Arziki ta Landan.
"Tun daga bayanan farko da aka samu kan matsanancin yanayi a 2018 (Guguwar Florence), an samu ɗaruruwan bincike da suka yi ƙoƙarin alakanta hakan da ayyukan ɗan Adam wato sauyin yanayi," kamar yadda ya fada wa BBC. "An ga alamar hakan saboda wutar daji da guguwa da tsananin zafi da fari da kuma ruwan sama kamar da bakin ƙwarya."
Wani rukunin masana kimiyya a sashen nazarin alaƙar yanayi da ake kira World Weather Attribution (WWA), sun wallafa wasu bayanai kan yadda za a alaƙanta tsananin yanayi da kuma sauyin yanayin.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga manyan marubutan, masaniyar yanayi 'yar Jamus, Friederike Otto ta Kwalejin Imperial, Landan, ta fada wa BBC cewa mutane da dama na sane da yadda ɗumamar duniya ke shafar yanayi, "akwai ƙarancin ilimi kan yadda hakan ke afkuwa a yankuna daban-daban."
Ita da abokan aikinta sun fayyace bambanci kan hayaƙi ko iskar da ke haifara da kansar huhu. Sun yi bayanin cewa a irin wannan yanayi, likitoci ba za su ce sigari ce ta haifar da kansar ba, sai dai tabbas za su ce ɓarnar da sigarin ta haifar ce ta ta'azzara lamarin.
"Shi ma sauyin yanayi ba zai iya hadassa wani yanayi ba, saboda kowane yanayi na da nasa dalilan da ke haifar da shi, amma ɗumamar yanayi kan shafi girma da kuma yadda wani lamari ya faru. Sannan kuma zai iya nuna girman yadda wani lamari ya shafi al'umma da dukiyoyinsu da kuma halittu," a cewarsu.
Ta yaya yake aiki?

Asalin hoton, Getty Images
Tsarin na amfani da lissafin kwamfuta don nazaratar wasu lamura biyu. Na farko na duba yadda yanayin yake a yanzu, ciki har da ɗumamar yanayi da ayyukan mutane ke haifarwa.
Lamari na biyu na bincikawa don raba tasirin hayaƙi mai gurɓata muhalli da kuma gano yanayin da ake ciki kafin samun juyin juya halin masana'antu na Industrial Revolution.
Sai kuma masana kimiyya su auna yawan adadin da irin wannan matsanancin yanayin ya faru a lamurran biyu - yayin da kuma kafin a samu ɗumamar duniya.
Idan suka haɗa lissafin, za su iya cewa idan wani abu ya faru sau uku a lamarin farko, to akwai yiwuwar ɗumamar duniya kan sa abin ya sake faruwa sau uku.
'Sauyin yanayi na da alaƙa da dukkan matsanantan yanayi'

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai kuma a aikace, tasirin da sauyin yanayi ke yi ga matsanantan yanayi ya bambanta sosai.
"Saboda ɗumamar duniya, dukkan matsanantan zafi da ake fuskanta sun tasirantu ne da sauyin yanayi," in ji Dr Otto.
"Idan muka duba matsanancin zafind da aka yi a Siberia a 2021, mun gano cewa sauyin yanayi ne ya haifar da shi kuma ba zai faru ba ba don sauyin yanayi ba," a cewar Dr Otto "yayin da kuma muka duba matsanancin zafin da suka faru a Turaia a 2019, a wasu yankunan na Birtaniya, an samu yiwuwar samun matsanancin yanayi sau biyar ko fiye."
Rahoton masana a WWA ya ce za a iya samun ruwan sama cikin sauri yayin da kuma za a fi samun laima tare da iska mai ɗan zafi.
Sai dai kuma, game da sauran lamurra kamar guguwa, da ambaliya, da wutar daji, abin tambayar shi ne ko sauyin yanayi ya taka rawa wajen faruwarsu.

Asalin hoton, Getty Images
Nazari biyu cikin ɗaya

Asalin hoton, World Attribution Initiative
Labarin da Dr Otto ya bayar game da alaƙar yanayi na komawa ne ga matsanancin zafi da aka yi a binin Moscow na Rasha a 2010.
"A lokacin, ba a amsa tambayar ko sauyin yanayi na da alaƙa da shi ba."
A wajen 2012, ta samu wasu maƙaloli biyu game da lamarin. "Ɗaya ya ce sauyin yanayi ne ya sa za a iya samun sa sau biyar, inda kuma ɗayan ya ce Allah ne ya yi ikonsa. Da na karanta sai na tambayi kaina: ta yaya lamurran biyu za su zama ikon Allah kiuma a lokaci guda sauyin yanayi ya haifar da yiwuwar samuwarsa sau biyar?
"Hasali ma suna tambayar abubuwa mabambanta da juna."

Asalin hoton, Getty Images
"Idan muna magana kan sauyin yanayi, akasari muna magana ne kan ɗumamar duniya da matsanancin zafi kuma hakan wasu matakai ne da ba a gani da ido," a cewar Dr Otto.
"Mutane na fuskantar sauyin yanayi ta hanyoyi daban-daban. Idan kana da arziki da kuma ƙerarren gida, to ka samu garkuwa daga zafi da kuma ambaliya. Abin da ke faruwa shi ne waɗanda abin ya fi shafa su ne ke shan wuyar sauyin da aka samu a yanayi."
'Sabawa yadda ya kamata'

Asalin hoton, Getty Images
Dr Otto na fatan bincikenta zai yi amfani ta hanyoyi da dama.
Wasu lokutan misali, rahotannin hukuma kan alaƙanta annoba da sauyin yanayi amma masana kan ce yana da kyau a guji alaƙanta kowane hauhawar zafin yanayi da ɗumamar duniya.
"Babban amfanin shi ne," a cewar Dr Otto, "taimaka mana wajen fahimtar asarori da kuma ɓarnar sauyin yanayi idan aka kwatanta da yanayin da aka saba da shi kawai. Yayin da muke da masaniya kan yawan hayaƙin da ake fitarwa, ba mu da ƙididdiga kan matsalar. Nazarin alaƙa kan ba mu damar ganowa da kuma sabawa da shi yadda ya kamata."











