Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan Afirka ta Kudun da ke gaban kansu wajen korar baki daga kasar
- Marubuci, Daga Lebo Diseko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Johannesburg, South Africa
Shugaban Afrika Ta Kudu ya ce ya matuƙar damuwa da cin zarafin da ake yi wa 'yan kasashen ƙetare da ke aiki a ƙasarsa.
Wani babban ƙalubale ne da ake fama da shi a birnin Alexandra, wanda yana daya daga cikin inda aka samu matsalar nuna kin jinin baƙi a 2008. Wasu 'yan ci-rani da yawa sun bayyana wa BBC cewa suna rayuwa ne cikin firgici.
"Su bakwai ne suka zo nan a karon farko. Sun sa mun kwanta a ƙasa mu duka. Sun ɗauki injinanmu da abin busar da gashi da kuma wasu mayukan fesawa.
Ba mu da wani zaɓi illa mu bar su su tafi sakamakon suna ɗauke da bindigogi".
Za mu kira shi David amma ba sunansa ba ne na gaskiya, yana zaune a kusa da ni cikin tsoro a shagon askinsa da ke birnin Alexandra.
Dan kasar Mozambique yana duba wani rauni a hannunsa lokacin da yake mini wannan jawabin, inda yake cewa an kai masa hare-hare masu yawa saboda shi dan kasar waje ne kawai.
David ya ce ƴan Afrika Ta Kudu ne suka kai masa hare-haren, kuma ko wanne lokaci bukatarsu guda ce, cewa sai ya bar musu ƙasarsu.
"Suna ce mana dole mu bar musu ƙasarsu, mu rufe kasuwancin da muke yi, amma ni ban san inda za ni ba," in ji shi.
'Yar rumfar da ke zaune cikinta a matsayin shagon askinsa bai kai tsayin mita biyu ba, amma a bayyane yake cewa itace farin ciki da jin dadin David.
Akwai hotunan kitso da aski iri-iri a jikin bangon shagon, a gefe daya kuma makanar askinsa da 'yan sauran kayan aikinsa ne cikin wani kwando.
Dan kudaden da yake samu a nan su yake aikewa iyalansa da ke Mozambique. Amma ya ce a shirye yake ya yi komai domin ya samar musu rayuwa mai kyau.
"Matuƙar iyalaina suna ci suna ƙoshi komai ya yi daidai a wurina," in ji shi.
"Za su iya kashe ni a kowanne lokaci. Ban san me zai faru ba",
Rikicin da aka samu a tsakanin 'yan Afrika Ta Kudu da mazauna Alexandra ya sanya ana zaman tsoron barkewar wani rikicin nuna kin jinin baki a kasar.
Daga nan ne aka fara samun rikicin nuna ƙin jinin baki a 2008 da kuma daga baya ya fantsama sauran yankuna.
A fadin kasar baki daya, an kashe 'yan ƙasashen ƙetare a 2021 ninki uku na waɗanda aka kashe a rikicin baya, kamar yadda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Afrika ta bayyana.
Batun aiki da samun damar kasuwanci su ne manyan abubuwan da ƴan kungiyar Alexndra Dudula suka sanya a gaba. Dudula na nufin "tura abu baya" ko kuma "kora abu waje" da yaren Zulu.
Ta rufe shaguna da kantuna masu yawa da ta yi ikirarin ana gudanar da su ba bisa ka'ida ba. Mutane kamar su David na cewa 'yan kungiyar Dudula ne suke kai irin hare-haren.
Mun yi ƙoƙarin jin ta kowanne ɓangare, inda muka tattauna da wasu ƴan kungiyar Dudula, ko da muka je mun tarar suna shirin fita aiki, na abin da suka kira duba takardun ƴan cirani.
Na tambayi daya daga cikinsu wadda ake kira Agnes Malatjie ko ta yaya ƙungiyar ke ɗaukar dokar a hannu.
"Ba za mu ƙyale wadannan sunayen da ka kira mana ba - ƴan sanya ido' - su karya mana tsarin kasarmu da abin da suke kira 'yan cinsu," in ji ta.
Ta zargi hukumomi da rashin aiwatar da dokar hana shige da fice ko kuma daukar mataki lokacin da aka kai wa 'yan Afrika Ta Kudu hari.
"Da gwamnati na yin abin da ya dace da ba murika yin wannan aikin sintirin ba.
"Ana cin zarafinmu, ana kai mana hare-hare ko a ranar 7 ga watan Maris 'yan kasashen ketare sun rika kai mana hare-hare da sandinda da kuma makamai. Don haka akwai abubuwan da suke bukatar a rika sanya ido a kansu sosai."
Alexandra na daya daga cikin matalautan birane a kasar.
Kusancinsa da arziki da kuma samar da ke da akwai sun dade suna jan hankalin sabbin zuwa, zuwa Johannesburg daga cikin kasar har zuwa nahiyar.
Amma ana kara samun matsin lamba kan albarkatun birnin da ke kara samun yawaitar mutane, don haka da yiwuwar a yi rikici tsakanin masu zuwa a kusa da mazauna garin da ake zagayewa.
Akwai wuyar bayani kan abubuwan da ke faruwa, in ji Dr Lufuno Sadiki, wata ƙwararriya a fannin nazarin laifuka a jami'ar Pretoria.
"Dukanmu muna son rayuwa mai kyau, kuma ba kowa ne ke samun wannan rayuwar da muke fata ba."
"Kamar wani madubi ne da zai nuna duka fushin da ke fuskarka. Rashin daidaiton ya bayyana a fuskarka.
"Abubuwan da ake bukata su ne, samun damar hawan titina masu kyau wanda kuma ba a iya samu. A lokuta da dama idan muka rasa abin fada sai mu fara kai duka".
John mai shekara 19 - shi ma dai ba sunan shi ba ne, ya ce an sha kai masa irin wadannan hare-hare tun bayan zuwansa Johannesburg daga Mozambique a bara.
Shi da abokansa suna da rumfa a gefen titi suna dama nama da gashi suna sayarwa a cikin gari.
Ya ce 'yan Afrika Ta Kudu daga kungiyar Dudula suna kai musu hari tare da sace musu kayayyakinsu.
"Lokacin da 'yan Dudula suka zo dauke da makamai suka yi mana duka. lokacin da suka zo dole su gudu su bar duka kayansu".
A wajen John burinsu shi ne, ya taimakwa iyalansa da ke Mozambizue. Yana ta fatan samun kudaden da zai iya sayan motarsa ta farko.
Yanzu mafarkinsa yana cikin ƙila wa ƙala.