The Talk: Abin da iyaye baƙar fata ke gaya wa ƴaƴansu don tsira daga harin farare a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Leire Ventas
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC, Los Angeles
"Zan fayyace maka a matsayina na uwar ƴaƴa huɗu baƙaƙen fata: maganar ita ce tsaron kai, kan abubuwan da za ka yi ka zauna a gida lafiya."
Reverend Najuma Smith-Pollard ta san batun sosai, wadda ta aiwatar ga ɗanta a Daniel, wanda ya mutu a 2018 yana shekara 24, kuma yanzu tana da ƴaya uku ƴan shekara 12 da 17 da kuma 18, wani lokaci kuma da ƴarta ƴar shekara bakwai a kudancin Los Angeles.
Ba tattaunawa ba ce da ake yawan yi, batu ne da ake ambata lokaci ɗaya, amma wanda ke ci gaba da wakana, da ke faruwa tsakanin iyalan bakaken fata a shekaru da dama.
"Tatattaunawa da ke ci gaba da gudana tsakanin iyaye da ƴaƴansu game da yadda ya kamata su kare kansu a rayuwa ta yau da kullum," in ji Smith-Pollard wadda take bayyana ƙwarewarta a matsayinta na malamar kirista kuma shugabar al'umma a wurin aikinta Cibiyar nazarin harakokin addini da al'adu a jami'ar Southern California (USC).
"A matsayina na uwar ƴaƴa bakaken fata da ke zama a birni, ina magana da su game da ƴan sanda da kuma masu laifi, domin akwai mutane makwabta waɗanda ba su da mugunyar aniya.
"Ina koya masu yadda za su yi mu'amula da jami'an tsaro da kuma rayuwa gaba ɗaya, a cewarta.

Asalin hoton, Getty Images
Wanda aka fi sani da "The Talk, shi ne da'awar yau da kullun na abin da masana ilimi ke kira launin fata da zamantakewar ƙabilanci, wanda fage ne na nazari a fannin ilimin zamantakewa da halayyar ɗan adam.
Akwai ɗimbin rubuce-rubucen kimiyya game da maudu'in da shirye-shirye kamar The Talk: Race in America da ake gabatarwa a kafar talabijin na PBS a Amurka.
Duk da haka, wannan gaskiya ne.
Kuma waɗanda suka yi magana da BBC (har da waɗanda suka ƙi amincewa) sun bayyana "The Talk" a matsayin wani abu mai ɗaci, wani nauyi da iyalan Amurkawa ƴan asalin Afirka da Latino suke haƙuri da shi.

Asalin hoton, Getty Images
"Yanzu da ake yawan samun rikicin wariyar launin fata, haka kuma dole mu fara faɗawa matasanmu cewa, ba za ku taɓa yarda da fararen fata ƴan shekara 18 ba," in ji Smith-Pollard.
Tana ba da misali da harin bindiga a ranar 14 ga Mayu da mutum 10 suka mutu a wani babban kanti a Bufallo, New York inda baƙaƙen fata suka fi yawa.
Ƴan sanda
"Tatattauna tsakaninta da babban ɗanta ta fara ne lokacin da ya kai shekara 13. Yana aji bakwai wasu suka kai masa hari a kan hanyarsa ta zuwa ɗakin karatu tare da abokin karatunsa.
"Dole na faɗa masa, lokacin da kai da abokinsa kuka fita, ka dinga kula da wanda kake tare da shi."
Wannan saƙon game matakan tsaronsa ana maimaita masa a duk lokacin da zai fita shi kaɗai, amma abin ya sauya bayan ya samu lasisin tuki.

Asalin hoton, Getty Images
"Lokacin da ya fara tuƙi dole na fara magana da shi game da abin da ya dace ya yi da kuma abn da bai dace ba, idan har ka yi karo da ƴan sanda," in ji ta.
Tattaunawar ta fara ne kamar haka, kamar yadda take tunawa: "Mun zauna a Los Angeles, ɓangaren kudanci.
Ba sai ka yi wani abu marar kyau ba kafin a kama ka. Za su iya cewa ka tsaya, su tuhume ka. Ya kamata ka san cewa kana da ƴanci."
Ta riga ta faɗa masa game da ƴancinsa lokacin da ya cika shekara 15, saboda kamanninsa -dogo kuma kakkaura, ya buga wasan ƙwallon Amurka tun yana shekara tara kuma yawanci mutane na ɗaukarsa mai yawan shekaru.
"Kada ka bari wani ya fara bincikenka ba tare da yana da sammaci ba. Ba dole sai ka amsa tambayoyi ba, domin kai yaro ne. Za ka iya kiran mahaifiyarka, ka sa su kira ni nan-take.
"Kada ka damu idan har suna son tafiya da kai ofishin ƴan sanda. Kada ka yi faɗa kuma kada ka gudu. Mahaifinka da ni za mu yi ƙoƙarin fitar da kai daga ko wace irin fitina."
"Ka fada masu sunanka kuma ka nuna masu katinka na shaida. Abubuwan da za ka ba su kenan, kuma ya fi dacewa su diba da kansu domin tabbatar da ba ka taɓa aikata laifi ba.

Asalin hoton, Getty Images
Alƙalumma
Domin gano asalin "The Talk" dole sai ka yi waiwaye a shekaru dama baya, al'adar da aka riƙe zamani da dama. Smith-Pollard ta tuna yadda kakanta, a lokacin da take girma a Mississippi a1940, aka ba ta shawarar kada ta bi layin wasu unguwanni.
Kamar sauran iyayen baƙaƙen fata, tana tsoron cewa idan har ba ta yi wannan batun ba, ƴaƴanta za su faɗa tarkon rikici na gama-gari da kuma rikici na ƴan sanda.
Abu mafi muni, za su iya ƙarewa kamar George Floyd, wanda bikin shekara biyu da wani ɗan sanda farar fata Derek Chauvin ya kashe a Minneapolis a ranar Laraba 25 ga watan Mayu.
Akwai alƙalumma da za su tabbatar da fargabar.
A yankin Los Angeles, inda Smith-Pollard ke zama da iyalinsa, aƙalla mutum 968 jami'an tsaro suka kashe tun 2000, kamar yadda alƙalumman binciken likita ya nuna. Kusan kashi 80 baƙaƙen fata ne ko Latino, kusan yawancinsu maza ne.

Asalin hoton, Getty Images
A matakin ƙasa, alƙalumman sun nuna akwai rashin daidaito a bayanan, a cikin wani kundin bayanai da sashen tantance bayanai na BBC ya gano.
Alƙalumman ƴan sanda kan harbin bindiga da jaridar Washington Post ke sabuntawa tun 2015, kashi 24 na sama da mace-mace 6,000, waɗanda suka mutu Amurkawa ne ƴan asalin Afrika.
Duk da haka rukunin bai wuce kasa da kashi 13 na yawan al'ummar ƙasar ba.
Ƴan sanda sun fi tsayar da Amurkawa ƴan asalin Afirka a yayin da suke tukin mota - fiye da kashi 20, a cewar alƙalumman bincike da aka gudanar a Jami'ar Stanford a 2020 da ya yi nazari kan ababen hawa miliyan 100 da aka tsayar.
Fargaba
"Ina fatan ba zan taɓa tattaunawa ba da ɗa na," in ji Judy Belk, shugaban wata cibiya ta (Cal Wellness) a California, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin da ke taimakon al'umma a jihar da ta mayar da hankali kan kare rikici da matsalolin lafiyar al'umma.

Asalin hoton, The California Wellness Foundation
Amma abubuwa sun sauya lokacin da ɗanta - like Smith Pollard - yana tsakanin shekara 12 zuwa 13.
"Muna zaune a Oakland a baya kuma ina aiki a San Francisco. ya roƙe ni na bari ya yi tafiya shi kadai. Na damu matuƙa, na fada masa: kada ka yi magana da wanda ba ka sani, ka kira ni da zarar ka sauka."
Ya bi umarninta, kuma lokacin da suka hadu a San Francisco sun tattauna abubuwan da suka ba ta mamaki.
- Mama, ina ganin bai kamata ki dinga tunanin wani zai iya min illa ba. Ina ganin mutanen da ke cikin jirgin kasar suna ɗar-ɗar da ni a kusa da su.
- Me kake nufi?
- Ina ganin na tsorata wasu mata tsofaffi.
"Ban yi tunanin zai iya kaucewa irin wannan tunanin ba na wasu" in ji ta. Ta girma ne kudu inda ake nuna bambanci a Virginia, kuma tana fatan ba ƴaƴanta wani yanayi na daban ta ba su tarbiya a Califonia.

Asalin hoton, Getty Images
"A lokacin na fahimci ya kamata na taimaka masa ya fahimci yadda zai girma lafiya a matsayinsa na baƙar fata."
Karon farko da ƴan sanda suka tsayar da shi yana tuki, Belk ta ji daɗi mijinta na tare da shi. A North Carolina ne inda ɗanta yake karatun digiri.
Mahaihin ya ga dama ce ya koyar da ɗansa yadda zai tunkari yanayi, kamar yadda aka koyar da shi.
Ba a dade ba ƴan sanda suka harbe wasu bakaken fata Botham Jean da Atatiana Jefferson ƴan shekara 26 da 28 a gidansu.











