Bayani dalla-dalla kan zaben rabin zango na Amurka

Shekaru biyu ke nan da zabar Joe Biden shugaban kasar Amurka, masu kada kuri'a za su sake komawa rumfunan zaben a ranar 8 ga watan Nuwamba.

Zaben rabin zango da ake yi bayan shugaban kasa ya yi shekaru biyu kan karagar mulki, yayin da ake yin zaben shugaban kasa a kowacce shekara hudu.

Wa ake zaba?

Gwamnati da 'yan majalisu 535 ne ke wakiltar Amurkawa, wadanda ake kira mambobin majalisa.

Majalisar ta kasu kashi biyu, akwai majalisar dattijai da ta wakilai. Dukkan biyun ne suke haduwa domin yin dokoki.

Dari bisa dari na majalisar dokoki na da karfin fada a ji. Kowacce jiha a Amurka, komai kankantar ta sai ta aike da wakilai biyu. Ana zabar sanatocin ne kan wa'adin shekara shida. A kowacce shekara biyu kashi uku na majalisar na fuskantar zabe.

Majalisar wakilai kuwa na kunshe da mambobi 435. Kowanne mutum guda na wakiltar gundumar jiharsa, kuma suna yin wa'adin shekara biyu. Dukkan kujerun dai zabar su ake yi.

Ko akwai wata barazana?

A yanzu haka dai mambobin majalisar sun fito ne daga jam'iyyun Democratic da Republican.

Jam'iyyar Democrat ce ke iko da majalisun amma da matsakaicin rinjaye.

Kawo yanzu, hakan ta zama hanya mai sauki ga Shugaba Biden a matsayinsa na dan Democrat, yana samun komai cikin sauki.

Amma idan jam'iyyar Republican ta samu rinjaye a dukkan majalisun, za ta samu ikon mayar da hannun agogo baya ashirye-shiryen Biden.

Republican na bukatar samun karin kujeru biyar, domin kwashe masu rinjaye a watan Nuwamba mai zuwa. Ta ma fi kusanci da majalisar dattijai, inda aka kasa kujerun tsakanin jam'iyyun da ke cikinta. Amma a yanzu Democrat, na da iko saboda mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris tana da dama a kowanne yanayi.

Abin da Republican ke bukata domin yin nasara a zaben watan Nuwambar, shi ne karin kujera daya tilo.

Zaben fid da gwani ne ya ke nuna makomar 'yan takara a zabe mai zuwa, wanda kowacce jam'iyya za ta shiga a fafata a daukacin kasar baki daya a watan Mayu da Satumba.

Wadanda ake ganin za su fafata

  • Mehmet Oz, fitaccen mai fitowa ashirin talbijin da ake fi sa ni da suna Dr Oz, ana fatan zai zamo sanatan Pennsylvania karkashin jam'iyyar Republican
  • Sai dan jam'iyyar Republican JD Vance, marubutcin littafin, Hillbilly Elegy, zai fafata da dan ytakarar shugaban kasa a shekarar 2020 a Ohio
  • Sai tsohon dan sama jannatin hukumar Nasa da sojin ruwan Amurka, Kaftin Mark Kelly na neman sake lashe kujerar sanatan jihar Arizona wanda a shekarar 2020 din ya yi nasara karkashin Republican

Wane ne zai lashe zaben?

Tarihi ya nuna cewa jam'iyyar da ke rike da Fadar White House ta fi shan kaye a zaben rabin zango.

Alamu sun nuna ba lallai ne kuma Republican ta yi nasara ba.

A yanzu da Shugaba Biden ya samu daukaka da suna, da kuma samun kashi 50 cikin 100 na kuri'u a watan Agusta.

Ba lallai ya samu goyon bayan 'yan takara karkashin jam'iyyar Democratic ba.

Me hakan ke nufi ga Shugaba Biden?

Ko a yanzu, Mr Biden ya na bukatar goyon bayan dukkan 'yan jam'iyyar Democrat ldomin amincewa da duk wani kuduri da zai gabatar, kai hakan ma bai wadatar ba.

'Yan gani kashe nin Democrat sun yi wa kudurori da dama da shugaba Biden ya kai gaban majalisar kafar ungulu, ciki har da kudurin "Build Back Better", shirin dala tiriliyan guda ga ayyukan ci gaban al'umma da magance sauyin yanayi.

Gagarumin koma baya ga zaben tsakiyar wa'adi, wanda ka iya janyo shugaba Biden ya gagara gabatar da wasu sabbin dokoki.

Yawancin 'yan Republican sun nuna sha'awar yi wa harkokin gwamnatin Biden nazarin tsanaki.

Wannan ma na nufin watakil a kafa kwamitin bincike kan dukkan janyewar dakarun kawancen da Amirka ke jagoranta daga Afghanistan, da kuma danbarwar shugaban kasa da ta hada da dan shi Hunter Biden.

Tun 6 ga watan Junairu, lokacin da aka yi zanga-zanga ginin majalisar Capitol, aminci ya yi rauni tsakanin jam'iyyun biyu.

Sai kuma batun sanya takunkumin rufe fuska, da kiwon lafiya sun kara raba kawunan 'yan siyasar.

Raba iko da birnin Washington na nufin wata danbarwa da sai lokacin ya yi za a tantance ta.

Bayan wannan sai kuma me?

Da zarar an kammala zaben tsakiyar wa'adin, dukkan idanu da hankula za su karkata kan yadda zaben shugaban kasa na 2024 zai kasance a Amurka.

Watakil, tarihi ya kara maimaita kan shi, Shugaba Biden da Trump dukka sun nuna sha'awar tsake tsayawa takarar kamar yadda suka yi a 2022.

Sai dai ana sa ran sabbin 'yan takara za su kwararo domin a fafata da su.

Kamar dai zaben 'yan majalisa ranar 8 ga watan Nuwamba, kashi 36 cikin 50 na gwamnonin jihohi za su fafata a zaben. Cikin jihohi 36 'yan jam'iyyar Republican.

Idan aka fara gangamin yakin neman zaben shugaban kasa, gwamnoni kan koma marawa dan takarar jam'iyyarsu ba ya tare da kawar da ido kan jiharsu.

Yadda kawunan Washington ya rabu, da sabbin 'yan takarar gwamnoni ka iya kawo gagarumin sauyi a gangamin neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023 da 2024.