Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Joe Biden: Manyan jarrabawa huɗu da shugaban Amurka ya fuskanta kafin zama shugaban ƙasa
A ranar Laraba, 20 ga watan Janairun 2021 ne aka rantsar da Joseph Robinette Biden Jr wanda aka fi sani da Joe Biden a matsayin shugaban ƙasar Amurka na 46.
A rantsar da shi ne tare da Kamala Harris wadda ita ce mace ta farko kuma baƙar fata a tarihin ƙasar da ta fara kai wa ga irin wannan mukamin.
Mista Biden ya fuskanci ƙalubale daban-daban a rayuwarsa da kuma jarrabawa irin ta ubangiji.
Ga wasu daga cikin abubuwan da shugaban ya fuskanta a rayuwarsa da suka girgirza shi:
Mutuwar matarsa da ƴarsa a 1972
A 1972 bayan Biden ya lashe kujerar ɗan majalisar dattawa daga jihar Delaware ta Amurka, sai murna ta koma ciki bayan wani mummunan hatsarin mota da iyalin Joe Biden suka samu.
A dalilin hatsarin, ya rasa matarsa ta farko Neilia da kuma jaririyar ƴarsa Naomi. Duk a cikin hatsarin, akwai yaransa ƙanana wato Beau da kuma Hunter, amma su duk sun rayu bayan hatsarin.
Hasali ma Mista Biden ya sha ranstuwarsa ta kama aiki ne daga asibiti inda ƴaƴansa maza biyu da suka rayu ke jinya .
Kusan wata ɗaya ne kafin iyalin nasa su yi wannan hatsarin, Biden mai shekara 29 a lokacin wanda ɗan jam'iyyar Democrat ne ya zama mutum na biyu mafi ƙarancin shekaru da ya zama sanata a Amurka, inda ya doke wani ɗan Jam'iyyar Democrat wanda ya shafe wa'adi kan kujerar, kuma a lokacin mutane da dama sun yi zaton Biden ɗin ba zai iya lashe kujerar ba.
Mutuwar ɗansa Beau Biden a 2015
Beau Biden na daga cikin iyalin Trump da hatsarin mota ya rutsa da su a 1972 inda har mahaifiyarsa da ƙanwarsa suka mutu, sai dai shi kuma Allah ya yi masa tsawon kwana domin sai kusan bayan shekara 43 da afkuwar hatsarin Allah ya ɗauki rayuwarsa.
Beau ya mutu a 2015 yana mai shekara 46 da haihuwa. Ya mutu ne sanadiyar cutar daji ta ƙwaƙwalwa wadda ake kira brain cancer a Turance.
Mista Beau yana daga cikin matasa ƴan siyasa da ke tashe a Amurka, inda har yake da burin takarar gwamnan jihar Delaware a 2016.
Ko a yaƙin neman zaɓen Joe Biden, sai da yace mutuwar ɗansa Beau na daga cikin abubuwan da suka sa zai sake tsayawa takarar shugabancin ƙasa, inda ya ce gyaran ɓangaren kiwon lafiya na da muhimmanci, kuma ya yi alƙwarin zai sa a gaba idan ya zama shugaban ƙasa.
A 2016, Joe Biden ya yi niyyar tsayawa takarar shugabancin Amurka, sai dai mutuwar ɗansa Beau na daga cikin abubuwan da suka hana shi tsayawa takarar.
Ya bayyana cewa iyalinsa ba su daɗe da dawowa cikin hayyacinsu ba sakamakon mutuwar ɗan nasa.
Korar Hunter Biden daga Soja
A 2014, ne aka bayar da rahoton cewa an kori Hunter Biden daga aikin sojan ruwa, wanda shi ne ɗa ga Joe Biden na biyu bayan Beau.
Bincike ya nuna cewa an sallami Mista Hunter ne bayan ya faɗi a gwajin da aka yi masa na shan ƙwayoyi, wato an gano miyagun ƙwayoyi a jininsa.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa an ga alamun hodar ibilis a cikin jinin Hunter.
Wannan lamari dai ya tayar da ƙura musamman lokacin da Joe Biden ya yi muhawara da Donald Trump a bara, inda Trump ɗin ya zargi cewa an yi wa Hunter korar kare daga aikin soja.
Biden ya mayar wa Trump da martani inda ya ce ba a yi wa Hunter korar kare ba, amma lallai ya taɓa samun matsalar shan miyagun ƙwayoyi amma ya je asibiti kuma an magance matsalar, wadda ya ce akwai ta a gidan kusan kowa.
Yin I'Ina
Shugaba Biden ya yi fama da i'ina tun yana ɗan ƙaraminsa kuma hakan ya sa ya fuskanci wulaƙanci da zolaya daga wurin yara.
Sai dai ko da ya girma ya shiga harkokin siyasa, bai daina i'inar ba inda har wasu 'yan adawa a Amurka ke ganin cewa ba i'ina ba ce kawai ke damunsa, yana da wata matsala a ƙwaƙwalwa kuma ba zai iya shugabanci ba.
Sai dai Joe Biden ya sha bayyana cewa lafiyarsa ƙalau kuma ba shi da wata matsala a ƙwaƙwalwarsa.
"I'ina na matsalar ƙwaƙwalwa ba ce kuma ba ta auna kaifin basira. Bai dace a ce har yanzu ana yi wa masu i'ina dariya ba saboda cin fuska ne," a cewarsa.
Sau da yawa tsohon shugaba Donald Trump kan yi wa Biden inkiya da "Sleepy Joe" ma'ana "Joe mai magana kamar mai jin bacci."
Biden ya ce i'inarsa wani ɓangare ne na rayuwarsa da ba zai taɓa rabuwa da shi ba saboda yadda ya shafi rayuwarsa.
Ya ce a duk inda aka buƙaci ya yi magana a cikin mutane ya kan shiga wani hali saboda tsoron kar a yi masa dariyar i'inarsa.
Ya ce wannan matsala ta shafi rayuwarsa sosai har sai da ya koyi hanyoyin taƙaita bayyanar i'inar idan yana magana a bainar jama'a.
Duk da waɗannan ƙalubale da Biden ya fuskanta, a yanzu ya zama shugaban Amurka yana da shekara 78.
Wasu na iya ganinsa a matsayin wanda bai bari matsalolinsa sun hana shi cimma burinsa ba.
Kuma wannan na nuna cewa jarrabawa ta rayuwa kan zo wa kowa ta ɓangarori daban-daban kuma a kowane irin salo.