Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaƙin Rasha da Ukraine: Hanyoyin da Rasha ta bi wajen ƙulla ƙawance da ƙasashen Afirka
- Marubuci, Daga Ilya Barabanov
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Russian
Rasha na cia gaba da faɗaɗa tasirinta a yankin Afirka a 'yan shekarun nan da kuma bayan ta afka wa Ukraine tana mai fatan samun sababbin ƙawayen da za su tallafa mata ko kuma su zama 'yan ba-ruwana a wurare kamar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
Daga Libya zuwa Mali, Sudan, Kenya, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR), Mozambique da sauran wurare, Rasha na ci gaba da shiga lamura - wasu lokutan a harkokin soja inda take taimakawa wajen yaƙar masu iƙirarin jihadi da kuma 'yan tawaye.
A taron Kwamatin Tsaro na MDD, ƙasar Kenya wadda ba ta da kujerar dindindin, ta bayyana adawarta ƙarara ga hare-haren da Rasha ke kai wa Ukraine.
Sai dai har yanzu babu wata kururuwar Allah wadai da hare-haren daga nahiyar don goya wa Kenya baya. Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka ta African Union (AU) ta bayyana "damuwarta" game da abin da ke faruwa amma ba ta soki Rasha ba.
Afirka ta Kudu wadda ƙawar Rasha ce a ƙungiyar Brics, ta yi kira ga ƙasar ta janye dakarunta daga Ukraine amma ta ce har yanzu tana da ƙwarin gwiwar sasantawa ta hanyar difilomasiyya.
A gefe guda kuma, an ruwaito Shugaban CAR Faustin-Archange Touadéra yana goyon bayan Rasha bisa amincewa da 'yancin kai na yankunan Ukraine biyu, Donetsk da Luhansk, bayan sun ɓalle daga ƙasar.
Sai kuma a ranar Laraba, mataimakin shugaban gwamnatin soja ta Sudan, Mohamed Hamdan Dagalo, ya jagoranci tawaga zuwa Rasha a matsayin wata alama inganta alaƙa tsakanin ƙasashen.
Ɗaya daga cikin alamomin yadda alaƙa ke sauyawa a Afirka ta bayyana mako ɗaya da ya gabata kafin harin Rasha a Ukraine lokacin da aka kawo ƙarshen yaƙin da Faransa ke yi da mayaƙa masu iƙirarin jihadi.
Firaministan Mali Choguel Maiga ya tabbatar a wata hirarsa da France24 cewa ƙasarsa ta ƙulla yarjejeniya da Rasha ta harkokin soja. Amma ya ƙaryata maganar kamfanin soja na Rasha mai suna Wagner da ke aiki a ƙasar.
Wannan taimakon na Mali da kuma rahoton da aka samu na tayin da ƙasar ta yi wa gwamnatin soja ta Burkina Faso, ya nuna salon da Rasha take bi cikin shekara biyar da suka wuce na jaddada alaƙa da Afirka a hukumance da asirce.
A yunƙurinta na ci gaba da ƙulla alaƙa da Afirka, wani taro na 2019 da aka yi a birnbin Sochi na Rasha ya samu halartar wakilai fiye da 50 daga ƙasashen Afirka, ciki har da shugabanni 43.
Shugaba Vladmir Putin ya yi wa shugabannin jawabi yana mai faɗa musu cewa Rasha za ta goyi bayan sama musu 'yanci da kuma haɓaka tattalin arziƙinsu.
Amma akwai wata hanyar ta alaƙa; ba da tallafin tsaro ga wasu ƙasashen Afirka ta hanyar bai wa dakaru horo da tattara bayanan sirri da ba su makamai, har da shigar wasu sojojin Rasha a fagagen dagar Afirka.
Kamar yadda Mista Putin ya ce, akwai alaƙa ta tarihi tun lokacin Tarayyar Soviet (USSR), inda Afirka ta kasance fagen rigegeniya tsakaninta da Amurka.
Sai dai alaƙar Afirka da Rasha ba ta cikin na gaba-gaba tun bayan da USSR ta rushe a 1991. Amma daga baya Rasha ta ɗauki abin da muhimmanci lokacin da take son dawowa kan ganiya a siyasar duniya.
"Saboda takunkumai, Rasha na buƙatar ta samu sabuwar kasuwar vda za ta kai kayan da take ƙerawa," a cewar Irina Abramova, darakta a cibiyar nazarin Afirka da ke Rasha ta National Academy of Sciences.
Sai dai na buƙatar fiye da kasuwa - tana son kuma ƙarin tasiri a siyasar duniya.
A 2014, ta shiga yaƙin basasar Syria tsamo-tsamo, inda ta goyi bayan Shugaba Bashir al-Assad don ta nuna kuskuren da Turawan Yamma suke yi da kuma yadda za ta yi ta gyara shi.
Daga Syria sai ta matsa zuwa nahiyar Afirka.
Irina Filatova, farfesa a Jami'ar KwaZulu-Natal da ke Afirka ta Kudu, ya ce manufar Rasha a Afirka ita ce ta ayyana tasirin ƙasashen Yamma a matsayin gurɓatacce kamar dai a Syria.
Tana so ta tabbatar da cewa Turawan Yamma sun kasa kawo ƙarshen hare-haren masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.
Dakarun sojan hayar Wagner na Rasha sun fara ɓulla ne a CAR a 2017.
Daga sai dakarun Rasha suka biyo bayansu a matsayin masu ba da shawara. Yunƙurinsu shi ne su taimaka wa Shugaba Touadéra ya ci gaba da zama a kan mulki.
Haka nan akwia sojojin haya na Rasha a Libya da Sudan da Mozambique da Mali, kowanne da irin nasarar da suka samu.
Afirka ta zama dandalin kasuwancin makaman Rasha. Kusan rabin dukkan makaman da ke shiga Afirka na Rasha ne, a cewar hukumar da ke kula da safarar kayayyaki ta Rasha.
Ƙasashen Aljeriya da Masar ne suka fi sayan makaman, amma akwai sabbin kasuwanni a Najeriya da da Tanzania da Kamaru.
Kazalika akwai amfani a ɓangaren siyasar duniya. A jumlace, Afirka na da fiye da rabin jumillar ƙuri'a a Babban Zauren MDD kuma hakan zai iya zama wata hanya ta mgana da murya ɗaya a wasu hukumomin na ƙasashen duniya.
Wani rahoto da cibiyar Higher School of Economics ta wallafa a 2021 ya bayyana cewa ƙasashen Afirka za su kasance 'yan ba-ruwana game da abubuwan da Rasha ta aikata a baya.
"Babu wata ƙasar Afirka da ta saka wa Rasha takunkumi [bayan 2014]. Lokacin kaɗa ƙuri'a a MDD kan rikicin Ukraine, mafi yawan ƙasashen yankin sun zaɓi su zama 'yan ba-ruwana," a cewar rahoton.
Bayan afka wa Ukraine, idan ƙasashen Afirka suka ci gaba da zama 'yan ba-ruwana, za a iya cewa yunƙurin da Rashar ta yi ta yi a 'yan shekarun baya kwalliya ta biya kuɗin sabulu.