Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Volodymyr Zelensky: Shugaban Ukraine wanda ya musanya shaharar fim da ta siyasa
Lokacin da Volodymyr Zelensky ya fara bayyana a talabijin a matsayin shugaban kasar Ukraine, ya yi haka ne a matsayin dan fim cikin wani shirin talabijin na barkwanci mai farin jini.
Sai dai mafarkinsa ya zama gaskiya a watan Afrilun 2019 bayan da ya zama shugaban kasar a zahiri. A yanzu yana jagorantar kasar mai mutum miliyan 44 wadda ke fuskantar hare-hare daga Rasha.
A wasan talabijin mai suna Servant of the People (Bawan Jama'a), Zelensky ya taka rawar wani malamin tarihi a makaranta wanda ya zama shugaban kasa bayan da wani bidiyonsa ya bayyana a intanet yana kalamai masu zafi kan cin hanci da rashawa.
Bidiyon ya ja hankulan 'yan Ukraine, wadanda sun gaji da kwamacalar 'yan siyasar kasar.
Sai Volodymyr Zelensky ya saka wa jam'iyarsa ta siyasa sunan wasan talabijin din, wato Servant of the People, kuma ya rika yin gangami yana mika sakon tsaftace siyasar kasar da wanzar da yanayin zaman lumana a gabashin Turai.
Amma sai ga shi al'amarin ya sauya, bayan da Rasha ta tura dakarunta zuwa Ukraine, matsalar da ta jefa shugaban a tsakiyar rikici tsakanin yammacin Turai da Rasha.
Shugaban mai shekara 44 ya sami kansa a tsaka mai wuya, inda ya rika neman taimakon kasashen yammacin Turai yayin da yake bayyana bukatun Ukraine ga duniya, kuma yana kaucewa tayar da hankulan al'ummar kasarsa ba.
Mai sana'ar barkwanci
Hanyar da Zelensky ya bi ta zama shugaban kasa ba irin wadda 'yan siyasa suka saba bi ba ne.
An haife shi a birnin Kryvyi Rih kuma iyayensa Yahudawa ne. Volodymyr Zelensky ya halarci Jami'ar Kyiv National Economic University inda ya yi karatun lauya. Sai dai ya shahara a wasan barkwanci.
Tun yana matashi ya fara fitowa a cikin wani wasan barkwanci da ake haskawa a wata tashar talabijin ta Rasha. A shekarar 2003 ya kafa wani kamfanin hada fina-finan talabijin mai suna Kvartal 95.
Kamfanin ya rika fitar da wasannin barkwanci da aka rika haskawa a tashar talabijin ta Ukraine mai suna 1+1, wanda mamallakinta biloniya Ihor Kolomoisky daga baya ya mara wa yunkurin Zelensky na neman mukamin shugaban kasar.
A cikin shekarun 201o kuwa, ya fi mayar da hankali ne kan yin fina-finai kamar Love in the Big City (2009) da Rzhevsky Versus Napoleon (2012).
Bawan Jama'a
Wani rikicin siyasa da ya taso a shekarra 2014 ne ya share wa Mista Zelensky fagen zama shugaban kasa, bayan da aka kayar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Viktor Yanukovych mai alakar kut-da-kut da Rasha bayan da aka shafe watanni ana zanga-zanga.
Daga nan ne Rasha ta kwace yankin Crimea sannan ta mara wa 'yan awaren da ke yaki da gwamnati a gabashin Ukraine, yakin da har zuwa yau ana yinsa.
Bayan shekara guda, a watan Oktoban 2015, shirin Servant of the People ya yi fitowarsa ta farko a tashar talabijin ta 1+1, inda ya taka rawar wani mutum mai suna Vasiliy Goloborodk, wanda malamin makaranta ne da ya zama shugaban kasa a cikin wasan barkwancin, lamarin da daga baya ya zama tamkar mafarkin da ya zama gaskiya a rayuwar Mista Zelensky.
Ya kayar da shugaba mai ci Petro Poroshenko, wanda ya so ya nuna wa 'yan kasar cewa Zelensky sabon shiga ne a siyasa, duk da cewa masu zabe na kallon rashin kwarewar ta Mista Zelensky a matsayin abu mai kyau.
An zabe shi da gagarumin rinjaye inda ya sami kashi 73.2 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben kuma ana rantsar da shi a a matsayin shugaban kasa ranar 20 ga watan Mayun 2019.
Cikas a Donbas
Ya yi kokarin cika alkawarin da ya dauka na kawo karshen yakin da ake yi a gabashin Ukraine, wanda ya halaka mutum 14,000.
Da farko ya yi kokarin yin sasanci. Ya tattauna da Rasha da sakin fursunonin yaki da kuma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, wanda aka fi sani da Minsk Agreement tsakanin kasashen. Sai dai ba a bi matakan sau da kafa ba.
Shirin wanzar da zaman lafiya ya gamu da cikas bayan da Shugaba Vladimir Putin ya fara ba mazauna yankunan gabashin Ukraine fasfon Rasha.
Bayan wannan lokacin ne Mista Zelensky ya fara furta tsauraran kalamai kuma ya rika nuna goyon bayansa ga shigar da kasar cikin tarayyar Turai da kungiyar tsaro ta NATO, matakan da suka harzuka Shugaban Rasha.
Ya rika ziyartar sojojin Ukraine a fagen daga, kuma ya yi kokarin hada kan 'yan kasar bayan da ya ayyana wata rana ta musamman a matsayin ranar hadin kai ranar 16 ga watan Fabrairu.
Bayan da aka tambaye shi ko gargadin da Rasha ke yi wa kasar Ukraine zai sa ya sauya aniyarsa ta shigar da kasar kungiyar tsaro ta Nato, sai ya shaida wa BBC cewa abu mafi muhimmanci a matsayinsa na shugaban kasa, shi ne kar kasarsa ta fada hannun abokan gaba.
"Muna bukatar tabbaci da kariya. Ba kalmomi hudu ne kawai muke kallo ba. A garemu, NATO tabbacin samun tsaro ne."
Kokarin karfafa iko
Akwai kuma wani alkawurin da ya yi da ya kasa cikawa: wato alkawarin dakile karfin iko na siyasa da na tattalin arziki da manyan attajiran kasar Ukraine ke da shi.
Masu sukarsa sun rika nuna shakku kan alakarsa da Ihor Kolomoisky, wani attajirin da ya mara masa baya yayin da yake kokarin tsayawa takarar shugaban kasa.
Sai dai ya yi kokarin abin da ya kira "sare fiffiken attajiran".
Gwamnatinsa ta rika kai wa wasu fitattaun attajiran kasar hari, ciki har da jagoran 'yan adawa mai alaka da Rasha Viktor Medvedchuk, wanda ka yi wa daurin talala kan tuhumar da ake ma sa, ciki har da na cin amanar kasa wadanda ya kira "matsi na siyasa."
Sai kuma ya kafa wata doka da ta takaita karfin ikon attajiran kuma ta rage yawan walwalar da suke da ita a fagen tattalin arziki, ciki har da hana su ba jam'iyyun siyasar kasar kudade.
Sai dai masu sukan salon mulkinsa sun rika kallon matakan yaki da cin hanci da rashawa da yake dauka a matsayin na wasan kwaikwayo, kuma suna cewa yana neman Amurka ta yaba ma sa ne kawai.
Zelensky ya taka rawar da ta dame shi
Domin ya sami taimako daga Amurka, sai da Mista Zelensky ya yi wasu abubuwan da bai so ba.
A watan Yulin 2019, Shugaba Trump na Amurka kuma dan jam'iyyar Republican ya kira Mista Zelensky kuma ya bukace shi ya "taimaka masa".
Mista Trump ya bukaci Mista Zelensky ya binciki wasu tuhume-tuhume na cin hanci kan Mista Biden, wanda a lokacin shi ne dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Democrat wanda ke kan hanyarsa ta lashe zaben.
Idan ya yi abin da Mista Trump ke so, Mista Zelensky zai sami damar ganawa da Trump a Washington kuma zai ba shi taimakon makaman yaki.
Bayan da wani ya fallasa abubuwan da Mista Trump ya bukata daga Mista Zelensky a tattaunawar wayar tarho da shugabannin biyu suka yi.
An zargi Mista Trump da matsa wa shugaban na Ukraine ya nemo bayanai kan abokin hamayyarsa na siyasa domin a yi masa sharri, wanda laifi ne karkashin dokokin Amurka.
Mista Trump ya kafe cewa bai aikata wani abin da ake kallo a matsayin laifi ba, inda shi kuma Mista Zelensky ya musanta cewa sun kulla wata yarjejeniya tsakaninsu.
Bayan wannan lokacin ne 'yan Democrat suka tsige Mista Trump, sai dai an wanke shi daga baya a majalisar dattawan kasar.
Badakkalar takardun Pandora
Mista Zelensky ma bai tsira daga badakkalar da ta shafi Mista Trump ba.
A watan Oktoban 2021, an bayyana sunansa cikin takardun sirrin nan da aka bankado na Pandora Papers, wadanda suka bayyana yadda wasu shugabanni da attajirai suka sace kadarorin kasashensu kuma suka boye su a wasu kasashen ketare.
An bankado cewa Mista Zelensky da wasu mukarrabansa na kut-da-kut sun amfana da wasu haramtattun kudaden da wasu kamfanonin kasashen waje suka basu.
Sai dai Mista Zelensky ya ce babu wata hujja cikin takardun kuma ya ce babu wani cikin ma'aikatan kamfaninsa, Kvartal 95 ko shi kansa da suka halarta kudaden haram.