Rikicin Ukraine: Shin akwai wadanda Putin ke jin maganarsu a duniya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Olga Ivshina da Kateryna Khinkulova
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian Service
A 'yan makonnin da suka gabata, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya dauki wasu muhimman matakai wadanda ba kawai kan Ukraine da Rasha tasirinsu zai tsaya ba, har ma ga sauran kasashen duniya. Ko wa ya tuntuba yayin da yake yanke wannan hukuncin? Shin me ya haifar da wannan matakin sojin - ko tasirin kungiyar nan ta 'siloviki' ta shugabannin hukumomin tsaro da ministoci mai karfin fada a ji ne?
Ana iya cewa Rasha kasa ce da shugabanninta ke da dimbin karfin fada a ji. Shugaba Vladimir Putin ne ke rike da yawancin iko a kasar, kuma shi da kansa ke yanke hukunci kan dukkan muhimman abubuwan da suka shafi kasar.
Sai dai duk da haka, yana tuntubar kungiyar jagororin hukumomin tsaron kasar, musamman wadanda ya dade da saninsu kuma ya amince musu.
Akwai wasu fitattun hukumomin tsaro a Rasha da ake kiransu "siloviki" (daga "sila" - wato karfi da Rashanci). Shi kansa Vladimir Putin a cikin irin wadannna hukumomin tsaron ya fara aiki - wato a KGB, wadda a shekarun da suka biyo bayan rushewar tsohuwar Tarayyar Soviet hukumar ta zama Russian Federal Security Service ko FSB. Kungiyar siloviki ta fara samun daukaka tun bayan da Putin ya dare kan karagar mulki.
Manyan abubuwa biyar
Ana yanke muhimman shawarwari a bangaren tsaro a Rasha yayin tarurrukan kwamitin tsaro na kasar.
Cikin kwamitin akwai manyan jami'an "siloviki" - kamar jagororin hukumar leken asiri ta FSB da na leken asirin kasashen waje da ministocin cikin gida da na harkokin da kasashen waje, da kuma firaiministan kasar da shugabannin majalisun kasar biyu. Mambobin wannan kungiyar su talatin ne.

Asalin hoton, Getty Images
Sakataren kwamitin tsaron Nikolay Patrushev, wanda shi ne shugaban hukumar leken asiri ta FSB, da Alexander Bortnikov da shugaban hukumar leken asirin kasashen ketare Sergey Naryshkin duka sun san Valdimir Putin tsawon gomman shekaru. Sun yi aiki tare da shi a birnin St Petersburg, wanda a baya sunansa Leningrad a shekarun 1970.
Baya ga wadannan jami'an, ministan tsaro Sergei Shoigu da ministan harkokin waje Sergei Lavrov wadanda su ne mutum biyar da suka fi kusanci da Shugaba Vladimir Putin kuma ya fi amincewa da shawarwarinsu idan yana son yanke hukunci kan muradun Rasha.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai ba mamaki a ce mafi kusanci ga Putin shi ne Sergei Shoigu, ministan tsaron Rasha, wanda kuma ke kula da hukumar leken asiri ta soji ta GRU, wadda ake tuhumar jami'anta da saka wa Sergei Skrypal (tsohon jami'in leken asirin Rasha) guba a Birtaniya a 2018, da kuma gubar da aka sanya wa dan adawan nan Alexei Navalny a Siberia a 2020.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban FSB Alexander Bortnikov ya taba aiki tare da Putin a ofishin KGB na Leningrad. Ya zama shugaban FSB a 2008, inda ya maye gurbin Patrushev.
Yana da kwarewa ta gomman shekaru a fagen leken asiri. Hukumar FSB na da iko kan sauran hukumomin tsaron kasar, kamar ma'aikatar harkokin cikin gida da ofishin mai shigar da kara.
FSB na da dakarunta na musamman, cikinsu akwai zaratan sojojin rundunonin Alfa da na Vympel.

Asalin hoton, Getty Images
Shi kuma ministan harkokin waje Sergei Lavrovna hannun riga da Bortnikov. Yana cikin jami'an diflomasiyya mafi dumbin kwarewa, kuma tun 2004 yake rike da ma'aikatar harkokin waje - kusan shekaru 20 ke nan. Kuma duk da cewa bai taba yin aikin leken asiri ko halartar makaranta daya da Putin ba, ana cewa Shugaban na Rasha na ganin girman sa sosai.
Kamar Bortnikov da Patrushev, shugaban hukumar leken asirin kasashen waje Sergei Naryshkin ya taba yin aiki tare da Vladimir Putin a Leningrad. Kuma wadanda suka san Naryshkin na cewa mutum ne mai biyayya matuka ga Putin.
Kwamitin tsaro: Mazaunin iko a Rasha
Taron baya bayan nan na kwamitin tsaron, wanda a ciki aka tattauna bukatar amincewa da "jamhuriyoyi" nan biyu na gabashin Ukraine su zama, wanda ya bayyana ainihin yadda kwamitin tsaron yake aiki.
Wakiliyar BBC a gabashin Turai Sarah Rainsford ta bayyana taron kwamitin a matsayin na kwaikwayo, wanda aka shirya wa kowa rawar da zai taka da abin da zai ce.
"Manyan jami'an Rasha sun zauna a zagaye a gaban Vladimir Putin, kuma ana kiransu daya bayan daya domin su tsaya a gaban na'urar magana domin su sanar da shi abin da ya ke son ji," inji ta.
Taron ya kuma haska irin ikon da Vladimir Putin ke da shi kan mambobin kwamitin tsaron da kuma yadda yake da iya cin fuskarsu a bainar jama'a - sannan ganin cewa alakarsu da shi dadaddiya ce, ba su da wurin buya idan matsala ta kunno kai.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa shugaban hukumar leken asirin kasashen waje Sergei Naryshkin dadadden abokin Shugaba Putin ne, wannan bai hana shugaban cin fuskarsa a bainar jama'a ba, saboda bai "fito fili ya yi bayani ba" yayin da yace a sake ba "kawaye na yammacin Turai" wata dama kafin a amince da bukatar yankunan gabashin kasar Ukraine da ke son ballewa daga kasar.
Wadannan kalaman sun fusata Putin, wanda ya matsa wa Naryshkin ya bayyana goyon bayansa a gaban kowa, matakin da ya furta nan take amma da gani ya razana da abin da Putin yayi ma sa.
Sai dai a fili yake cewa sauran mambobin kwamitin tsaron ba sa fuskantar irin wannan cin fuskar da Naryshkin ke fuskanta.
Ministan tsaro Shoigu da ministan harkokin waje Lavrov da shugaban FSB Bortnikov ne kawai mambobin kwamitin mai mambobi 30 da aka ba damar yin magana sau biyu yayin wannan tattaunawar.
Wani abu da ya ja hankula kuma shi ne yadda aka haska taron a talabijin - domin yawanci a boye ake gudanar da shi.
Sauran ma su bayar da shawara

Asalin hoton, Getty Images
Ana kuma cewa baya ga shugabannin hukumomin tsaron Rasha da ministan harkokin waje, Mista Putin na tattaunawa wasu fitattun 'yan Rashar da ke ciki da wajen gwamantin kasar.
Wani mai nazarin harkokin siyasar kasar Yevgeny Minchenko ya dade yana nazarin masu hannu da shuni na kasar. Yana kuma tattara bayanai kan makusantan Vladimir Putin akai-akai, wanda yake kira "Politburo 2.0".
A wani rahoto da ya fitar kwanan baya, Minchenko ya lissafa sunayen Magajin Garin Moscow Sergei Sobyanin da kuma shugaban kamfanin mai na kasar Igor Sechin cikin makusanta na musamman na shugaban kasar.
Akwai kuma attajiran biloniyoyin nan 'yan uwan juna Boris da Arkady Rotenberg da aka ce makusantan Vladimir Putin ne, domin tun yana yaro ya san su kuma ya amince da su. Suna cikin mutanen da aka bayyana cikin wadanda Birtaniya ta kakaba wa takunkumi. A shekarar 2020, mujallar Forbes ta ayyana su a matsayin 'yan gida daya da suka fi kowa kudi a kasar.

Sauran masu bayar da shawara

Asalin hoton, Getty Images
Ana kuma cewa baya ga shugabannin hukumomin tsaron Rasha da ministan harkokin waje, Mista Putin na tattaunawa wasu fitattun 'yan Rashar da ke ciki da wajen gwamantin kasar.
Wani mai nazarin harkokin siyasar kasar Yevgeny Minchenko ya dade yana nazarin masu hannu da shuni na kasar. Yana kuma tattara bayanai kan makusantan Vladimir Putin akai-akai, wanda yake kira "Politburo 2.0".
A wani rahoto da ya fitar kwanan baya, Minchenko ya lissafa sunayen Magajin Garin Moscow Sergei Sobyanin da kuma shugaban kamfanin mai na kasar Igor Sechin cikin makusanta na musamman na shugaban kasar.
Akwai kuma attajiran biloniyoyin nan 'yan uwan juna Boris da Arkady Rotenberg da aka ce makusantan Vladimir Putin ne, domin tun yana yaro ya san su kuma ya amince da su.
Suna cikin mutanen da aka bayyana cikin wadanda Birtaniya ta kakaba wa takunkumi. A shekarar 2020, mujallar Forbes ta ayyana su a matsayin 'yan gida daya da suka fi kowa kudi a kasar.