'Yadda na fada tarkon soyayyar yaudara ta intanet’

Asalin hoton, YZABEL DZISKY
- Marubuci, Daga Cagil Kasapoglu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Soyayya kan zama mai yaudararwa. Ita kanta soyayyar da ake yi a fili wato ƙeƙe-da-ƙeƙe ta kan zo da wasu abubuwa a ɓoye, da kuma bacin rai matuka.
Amma a duk lokacin da ka fara soyayyar kai kadai ta hanyar duniyar fasahar zamani, soyayyar da kake ji a ran ka ta kan shiga cikin hadari na gamuwa da matukar bacin rai.
Wannan shi ne abinda ya faru da Yzabel Dzisky, wata Bafaranshiya mai shirya fina-finai wacce duniyar soyayyar shafin intanet ta rudar, da ta kai ta ga fadawa cikin tarkon yaudara.
Ta shaida wa BBC yadda ta fada tarkon soyayya da wani mayaudarin shafin yanar gizo, da yadda yaudarar ta bar ta cikin tsananin bacin rai, da kuma yadda ta yi kokarin gano gaskiyar da take fatan za ta samar mata da warakar bacin zuciyar da ya same ta.

A shekarar 2017, lokacin Yzabel na da shekara 46, kana ba ta da aure kuma tana neman yin wani shirin talabijin kan manahajojin hada soyayya.
Burin shi ne a yi hira da mutane daban-daban kana a duba wadanda za su iya bayar da gudumawa.
Amma kuma har ila yau burin wannan shiri da alamu kamar wata dama ce ta samar wa kan ta masoyi.
"Kawayena da ba su da aure na fada min abubuwa game da duk wasu labaran soyayya na ban dariya da kuma soyayyar da suka yi ta hanyar irin wadannan manahajoji.

Da farko, na dauka cewa zan kawai yi hira da da mutane ne. Amma kuma yadda na dauka muddin mutane za su iya samun masoya ta wannan hanyar, me yiwuwa nima zan samu,'' ta ce.
Ta samo shafin wani kyakkyawan mutum.'Tony' (Colby) ne - akalla wannan shi ne sunan shi da zan fara da shi - wani likitan fida a birnin Los Angeles amma yana shirin komawa kasar Faransa nan ba da dadewa ba.
Ta fara mataki da farko, sun yi ta tattaunawa har na tsawon sama da mako daya.
"Ya yi magana game da tarihin rayuwarsa, kana ina fada masa nawa. Abin mamaki, sunayen karnukanmu da 'ya'yanmu mata kusan daya.

Asalin hoton, Getty Images
"Mata kan so irin wannan arashi, don haka wannan labarin soyayya ya dauki hankalina."
Mataki na biyu kuma ta bukaci ganinsa da hanyar kiran waya da bidiyo.
A ranar da suka fita yawon dare da kawayenta, Yzabel ta kira'Tony' ta wayarta kuma a cikin mitni 10 da suke magana ta bidiyon ta nuna wa kawenta fuskarsa.
Kai ne wanda motsawa sosa a cikin zagayen hoton bidiyon da ke kan fuskar karamar wayar salular.

"A duk lokacin da kake kiran waya a bidiyo, a lokuta da dama ka fi mayar da hankali ne wajen kallon kanka da yadda za ka yi kyau.
A maimakon mayar da hankali kan mutumin da kake wayar da shi, don haka ban mayar da hankalina sosai kan koma iba," Yzabel ta tuna.
Sun cigaba da tuntubar juna ta hanyar sakonni da gajerun kiran bidiyo har sai bayan da kwatsam 'Tony' ya daina tuntubarta ba tare da bayar da wasu dalilai ba.
Lokacin da ya dawo ya bata amsa, ya bayyana cewa shi ba Tony ba ne, sunansa na gaskiya. 'Murat'.

"Abin ya ba ni mamaki saboda wani arashi kuma sunan mijina da muka rabu ne Murat. Ya bayyana cewa shi dan kasar Turkiyya ne kuma yana zaune a Istanbul. Ban ji bacin rai ba ma, mamaki akwai na yi.
"Lokacin da na tambaye shi dalilin da ya say a sauya sunansa, sai y ace saboda ya fitone daga tushen yankin Gabas ta Tsakiya (Larabawa).
''Amma akwai lokacin da ya kira ni cewa yana Shanghai don sayen kayan aikin likita.
"Ya ce katin cirar kudinsa bay a aiki, kana ya nemi taimako na - yana bukatar in aika masa a euro 3,000.
"Bayan haka, 'Murat' y ace, zai tashi zuwa birnin Paris inda zai yi tozali da Yzabel.

Asalin hoton, Getty Images
Ta yi matukar mamakin yadda sanannen likitan fida zai bukaci kudi a wurinta, sai ta yi magana da kawayenta game da haka.
Sun fara zargin wani abu, amma ta yanke shawarar aika masa da euro 200 ta hanyar aikewa da sakon kudi ta intanet.
Da ranar ta zo, sai Yzabel ta cika da zumudin ganin shi a fili a karon farko.
"Na je filin saukar jiragen sama, Na sha jira…amma ban gan shi ba..''

Asalin hoton, YZABEL DZISKY
Yzabel ta dan yi shiru ta ja dogon numfashi lokacin da ta ke maganar filin saukar jiragen sama.
"Na yi kokarin sake tuntubarsa, baya daukar wata. Kana kwana biyu shiru kake ji. Raina ya yi matukar baci - me yasa ya ki daukar waya?''
***Murat ba shi ne sunansa na gaskiya ba - mun boye ne don nema masa kariya kamar yadda ya nema.

Menene 'Catfishing' da kuma hanyoyin kaucewa daga fadawa ciki?
'Catfishing' shi ne idan wani a bude shafin intanet na karya don yaudarar mutanen da ke son samun masoya, akasari don su karbi kudi daga gare su.
'Yan sanda a Birtaniya sun yi gargadi kan masu zambar soyayya ta intanet da cewa akasari su kan yi gagarumin abu don samun amincewar wadanda suka fada tarkonsu wajen nuna musu cewa suna son dangantakar soyayyar gaske ne.
Wani bincike da hukumar lura da harkokin kudi ta Birtaniya ta gudanar ya nuna cewa akwai kashi 20 bisa 100 na karuwar zambar soyayya ta shafin intanet.
Irin wannan zamba sun danganci aikewa da kudi ta bankuna daga tsakanin watan Janairu zuwa Nuwambar shekarar 2020 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabace ta.
A shekarar 2019, irin wadanna bincike ya gano cewa kashi 27 bisa dari na wadanda suka yi amfani da shafukan hada soyayya sun fada tarkon mayaudara.

Don kaucewa fadawa tarkon masu zambar shafin intanet na soyayyar:
Yi tambayoyi da yawa. Kada kwai ka dogara da bayanan da wani ya saka a shafin intanet.
Yi amfani da shafin na intanet a matsayin wani abin duba wasu wurare na samun bayanai da shafukan sada zumunta na mutumin da kake mu'amala da shi.
Ka tattauna ta shafin hada soyayyar. Ka guji bayar da lamrak wayarka ta gaskiya ko adireshin email kafin ka fahimci wanda kake hudda da shi.
Ka da ka sake ka bayar da kudi. Idan wani ya tambaye ka kudi a shafin intanet na soyayya, kada ka aika masa.
Menene deepfake?
Deepfake wata kalma ce da ake amfani da ita a ko ina wajen kwatanta duk wani bidiyo wanda a fuskarsa ko an sauya ne, ko an yi wa faskwarima ta hanyar fasahar zamani.
Akwai manahajoji da dama da abubuwan faskwarima da ake amfani da su wajen sauya fuskoki a cikin hotuna da bidiyo.
Bayanai daga: BBC, Age UK, UK Finance, UK Police












