Madrid za ta sayar da Camavinga, Arsenal ta fara cinikin Lukeba

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta saurari tayin da za a yi a kan dan wasanta na tsakiya na Faransa, Eduardo Camavinga, mai shekara 23, a bazaran nan, inda kungiyoyi da dama na Firimiya suke nuna sha'awar sayensa. (Marca)
Arsenal ta fara tattaunawa da RB Leipzig a kan dan bayan kungiyar ta Jamus, Castello Lukeba, dan Faransa mai shekara 23. (L'Equipe)
Chelsea, da Liverpool da kuma Manchester United, na shirin gogayya a kan cinikin dan wasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Adam Wharton, mai shekara 22. (Football Insider)
Haka kuma Chelsea da Manchester United na wata gogayyar kuma da sauran kungiyoyi a kan matashin dan wasan gaba na Cologne Said el Mala, dan Jamus mai shekara 19. (Caughtoffside)
Aston Villa na gogayya da kungiyoyi da dama na Turai a kan zawarcin dan wasan tsakiya na Jamus da Borussia Dortmund Julian Brandt, mai shekara 29, wanda zai kasance ba shi da wata kungiya a bazaran nan. (Fichajes)
Watakila Newcastle ta sake haduwa da Elliot Anderson, mai shekara 23, wanda ya taso daga cibiyar horad da matasan 'yan wasan kungiyar, a bazara, ganin yadda dan wasan na tsakiya na Nottingham Forest da Ingila zai iaya maye gurbi, idan dan wasan tsakiya Bruno Guimaraes na Brazil ko kuma dan wasan tsakiya na Italiya Sandro Tonali, wani daga cikinsu ya bar kungiyar. (Teamtalk)
Mai tsaron ragar Liverpool da Brazil Alisson, mai shekara 33, ya zama wanda Juventus take fatan saye a bazara. (Gazzetta dello Sport)
A yanzu Manchester United da Liverpool ne kan gaba wajen zawarcin dan wasan gaba na gefe na RB Leipzig, Yan Diomande, mai shekara 19, bayan da Bayern Munich, ta fice daga masu neman dan wasan na Ivory Coast. (Christian Falk)
Manchester City na son ta tabbatar da ganin dan wasanta na tsakiya Phil Foden, na Ingila mai shekara 25, ya ci gaba da zama har bayan kwantiraginsa na yanzu, wanda zai kare a 2027, kuma kungiyar na son ganin ta gaggauta kulla sabuwar yarjejeniya da shi. (Football Insider)
A shirye Manchester United take ta biya kusan yuro miliyan 100, na ka'idar sayar da dan wasan gaba na gefe na Sifaniya Nico Williams mai shekara 23, daga Athletic Club. (Fichajes)
Liverpool na dab da sayen matashin dan bayan Scotland, da ake kodawa Dara Jikiemi, mai shekara 16, bayan da ya ki amincewa da yarjejeniyar shekara uku ta ci gaba da zama a Celtic. (Teamtalk)











