Abin da ya sa Senegal ta amince da tsauraran dokokin haramta auren jinsi

An outline of a man is seen behind a rainbow LGBTQ+ flag at a march. Stock photo from library, not taken in Senegal.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

    • Marubuci, Nicolas Négoce
  • Lokacin karatu: Minti 4

Majalisar dokokin senegal ta amince da sabbin dokokin haramta auren jinsi waɗanda suka tanadar ɗaurin shekara 10 ga wanda aka samu da laifin, tare da mayar da auren jinsi babban laifi a ƙasar.

Ƴan majalisar dokokin ƙasar 135 ne suka goyi bayan matakin, yayin da babu ɗan majalaisar da ya goyi bayan adawa da matakin, sai kuma ƴan majalisa uku da ba su kaɗa ƙuri'arsu ba.

Yanzu abin da ya rage shi ne sanya hannun shugaban ƙasar, domin batun ya zama doka.

Dokar, wadda alawarin yaƙin neman zaɓe ne na Shugaba Bassirou Diomaye Faye da firaminsitan ƙasar, Ousmane Sonko - an aike da ita majalisar ne, bayan kama wasu mutane da ake zargi da auren jinsi, wanda haramun ne ƙarƙashin dokokin ƙasar.

Shugaban ƙungiyar kare haƙaƙin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk ya ce ƙudirin ''abin damuwa'' ne inda ya yi kira ga shugaban ƙasar da kada ya zanya hannu.

Kakakin gwamnatin ƙasar ya yi watsi da sukar ƙasashen duniya game da ƙudirin, yana mai cewa an yi ƙudirin ne bisa muradun ƙasar Senegal.

"Mafi yawan al'ummar Senegal ba su amince da auren jinsi ba. Al'adunmu ba su yarda da shi ba don haka mun haramta su,'' a cewar Amadou Moustpha Ndieck Sarre.

Ƴan gwagwarmaya masu ra'ayin riƙau a ƙasar sun jima suna neman saka tsattsauran hukunci kan masu alaƙar auren jinsi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙungiyar 'And Sàmm Jikko Yi', wadda ke gangamin kare abin da ta kira kyawawan al'adun Senegal ya sha koira ga hukumomin ƙasar su samar da wasu dokoki masu tsauri don haramta auren jinsi.

Shugabannin ƙungiyar sun ce ya zama wajibi a samar da dokokin domin kare al'adu da addinin al'ummar Senegal.

to sai dai, ƙungiyoyin hare haƙƙi sun yi gargaɗin cewa matakin zai yi matuƙar nuna wariya da muzguna wa masu muradin auren jinsin marasa rinjaye a ƙasar.

Mai bincike kan kare haƙƙin bil'adam, Larissa Kojoué ya ce matakin canje-canje abin damuwa ne.

"Mayar da auren jinsi babban laifi tare da kama mutanen da ke hakan, ya saɓa wa dokokin kare haƙƙin bil'adama na duniya, ciki har da ƴancin daidaito da rashin nuna wariya.''

Ta ƙara da cewa matakan na da hatsarin fallasa mutanen da dama tuni ake tsangwamarsu da ''fargaba da tsoro.''

Alioune Tine, wadda ta samar da cibiyar Afrikajom mai nazari kan harkokin kare haƙƙin bil'adama ta shaida wa BBC cewa ''Idan da gaske ne ana tsoron gurɓata al'adu, to ai yana da kyaua a martaba doka ma.''

Haka wasu masu rajin kare haƙƙin bil'adama na nuna cewa auren jinsi wani ɓangare ne na rayuwa, don haka bai kamata doka ta haramta shi ba.

Yawanci alaƙar jinsi ɗaya akan ɓoye su ta wata hanya. Akwai ma mutanen da suka yi aure a cikin al'umma kuma har yanzu suna alakar auren jinsi saboda al'ada da al'adu a cikin wannan al'umma," shugaban ƙungiyar LGBTQ kuma likita na Senegal Charles Dotou ya shaida wa BBC .

Tsaurara dokokin na senegal na zuwa ne bayan jerin kamen da aka yi watan da ya gabata kan azargin auren jinsi.

Ƴansanda sun tsare mutum 12, ciki har da wasu manya kuma fitattun ƴanjarida a ƙasar.

Masu goyon bayan sanya tsauraran dokokin sun ce sun yi la'akari da damuwar yaɗa cutar HIV wajen amincewa da dokokin, kodayake binciken kimiyya ta jima da tabbatar da cewa kowace irin alaƙar jima'i na yaɗa cutar.

Masana sun yi gargaɗin cewa ƙara haramta auren jinsi ka iya jega masu alakar jinsi da ke da cutar HIV cikin kunya da tsangwama wajen samun kulawar lafiyar da ta dace.

An jima ana yaba waa Senegal kan ƙoƙarinta na daƙile cutar HIV.

Ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce tsakanin mutum 42,000 zuwa 44,000 ke ɗauke da cutar a faɗin ƙasar, lamarin da ya sa ta zama ƙasar da ke kan gaba wajen ƙarancin masu ɗauke da cutar a Yammacin Afirka.

Ousmane Sonko, tsohon jagoran adawar ƙasar, da ka naɗa matsayin firaminista a 2024 ya shaida wa ƴan majalisar cewa ƙudurin ya tanadin hukuncin tarar saifa 10,000 (dala 17,000), da ɗaurin shekara biyar zuwa 10 a gidan yari a ƙasar da Musulmai ke da rinjaye.

A shekarun baya-bayan nan ƙasashen Afirka sun yi dokoki masu tsauri kan auren jinsi.

A watan Satumban shekarar da ta gabata, majalisar Burkina Faso ta amince da ƙudirin haramta auren jinsi da dangoginsa, bayan Mali ta yi a 2024.

A 2023, Uganda ta amince da ɗaya daga cikin dokoki mafiya a duniya kan masu auren jinsi, inda ta amince da hukuncin ɗaurin rai da rai kan wanda aka samu da yin haka.

Haka ma Ghana na shirin sake gabatar da ƙudurin dokokin haramta auren jinis, wanda masu gwagwarmaya suka ce na barazana na haƙaƙin ɗa'adam da tsaro da kuma ƴanci.