Ƙasashen da suka haramta auren jinsi ɗaya a Afirka

Alaƙar jinsi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Majalisar dokokin Burkina Faso 9wadda ta ƙunshi wakilai waɗanda ba zaɓaɓɓu ba) ta amince da wata doka da ke haramta alaƙa ta masu jinsi ɗaya, kimanin shekara daya bayan majalisar zartarwar ƙasar ta amince da wani daftarin dokar iyali wadda ta haramta auren jinsi.

A ranar Litinin ne majalisar ta amince da gagarumin rinjaye kan yanke wa wanda aka samu da karya dokar hukuncin ɗaurin da zai iya kai wa na shekara biyar, kuma hakan ya zamo na baya-bayan nan kan hukunta masu alaƙar jinsi a nahiyar Afirka.

A baya ƙasar ta kasance cikin ƙasashe 22 daga cikin ƙasashe 54 na nahiyar Afirka da ba su haramta alaƙar masu jinsi ɗaya ba, abin da ake yanke wa masu yin sa hukuncin kisa a wasu ƙasashen.

A bara, ƙasashen Mali da Burkina Faso masu maƙwaftaka - wadanda dukkanin su ke ƙarkashin mulkin soji sun yi dakokin haramta alaƙar jinsi.

Najeriya ma na cikin ƙasashen nahiyar da suka samar da dokar haramta alaƙar jinsi.

A bara majalisar dokokin Ghana ta amince da dokar hukunta masu alaƙar jinsi, sai dai shugaban na wancan lokaci bai sanya hannu a kai ba.

Uganda ce ta fi kaƙaba doka mafi tsauri kan lamarin a tsakanin ƙasashen Afirka, inda za a iya yanke wa masu alakar jinsi daya ɗaurin rai da rai.

Latsa saman ƙasa domin ganin matsayarta kan auren jinsi.