Benue: Yadda 'likita' ya cire wa mace ƙwayayen haihuwa lokacin tiyata

Shekara uku da ta gabata, iyalan wata matashiya mai shekara 18 sun shiga ɗakin tiyata da burin cewa aikin da likita zai yi mata zai kawo karshen rayuwar ƙunci da ta shafe watanni tana yi - ba tare da sanin cewa zai ƙara jefa ta cikin masifa bane.

Aneh, (ba sunanta na gaskiya ba kenan) na da shekara 15 a lokacin da wani ma'aikacin ɗakin tiyata mai suna Agber Kwende ya yi mata aiki a wani asibiti mai suna Gemanen Health Clinic wanda ke a Ƙaramar Hukumar Gaav Konshisha da ke Jihar Benue a Najeriya.

Ana zarginsa da cire mata ƙwayayan haihuwa da kuma wasu muhimman sassan jikinta.

Kamar yadda mahaifiyar Aneh wato Mgbatuman Ianna ta bayyana, an je an yi hoton cikin ƴarta har sau bakwai kuma an ga bututun mahaifarta a tsuke wanda hakan ke nufin ba za ta iya haihuwa a rayuwarta ba.

Tiyatar Afendis

Mgbatuman Ianna mai shekara 46 wadda ita ce mahaifiyar Aneh ta bayyana cewa ta shiga cikin wata irin damuwa sakamakon irin wahalar da ƴarta take ciki.

Ta bayyana wa BBC cewa ciwon da ƴarta ke fuskanta ya soma ne tun a Mayun 2019.

A cewarta, a duk lokacin da Aneh ke al'ada, tana fama da matsanancin ciwon ciki.

Sakamakon ba za ta iya jure ganin kullum yarta na ta kuka ba a duk lokacin da take al'ada ba, sai ta tafi wani asibitin yankinsu mai suna Gemanen Health Clinic, Ageraga domin domin a duba yarta.

Daga nan ne sai mai asibtin ya ce akwai buƙatar su je Gboko domin yi wa ƴar hoto, bayan sun koma asibitin da sakamakon hoton da aka yi mata, sai ya ce mata sakamakon na cewa tana da ciwon Afendis haka kuma tana da wani ciwo a tattare da ƙwayayen haihuwarta.

Sai likitan ya saka musu ranar yin tiyatar haka kuma ya ranto musu kuɗi daga banki inda ya ba su domin su biya a yi mata tiyatar.

Sai bayan kwanaki a cikin Mayun 2019, sai likitan ya kira Kwende domin yin wannan tiyatar.

Sai dai a maimakon tiyatar ta kawo wa Aneh ƙarshen matsalar da take fuskanta, sai lamarin ya ƙara ƙazanta sakamakon kullum Aneh na cikin rashin lafiya.

Neman magani

Ganin cewa rashin lafiyar Aneh a kullum ƙaruwa take yi, sai mahaifiyarta ta shiga damuwa.

Sai ta ɗauke ta inda ta kai ta wani asibiti na daban domin yi mata gwaji da hoto domin gano me ke damunta.

Bayan an yi mata hotuna da dama da kuma zuwa wurin likitoci daban-daban, sai suka shaida mata cewa wurin da aka yi wa yarta tiyatar ya kumbura - sai ta yi ƙoƙarin tara kuɗi domin kai ta asibiti mai kyau.

Daga ƙarshe sai suka je asibitin St John inda aka yi mata sabon hoto wanda ya nuna cewa an cire mata ƙwayayen haihuwa.

Bayan haka ne rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Gboko suka kama likitan da ya yi wannan tiyatar da kuma mai asibitin.

'Shiga damuwa har abada'

Aneh ta bayyana cewa a karon farko da aka shaida mata wannan labarin, ta sha kuka kuma har malaman jinyar asibitin sai da suka taya ta kuka.

Ta bayyana wa BBC cewa ba ta ji daɗi ba kwata-kwata sakamakon har abada ba za ta iya haihuwa ba.

Ta ce a kullum tana rayuwa cikin ƙunci da ciwo.

A halin yanzu iyalanta na ta fafutika domin ganin an ƙwato mata ƴanci.

'Ƙurjin da ke ƙwayayen mahaifa kawai na cire, ban cire ƙwayayen ba - Kwende

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Benue ta kama Kwende kuma mai asibitin, Joseph Ugoh ya musanta aikata duk wani laifi da ya shafi hakan.

Agber Kwende aikin tiyata yake yi.

A yayin wata hira da BBC, ya ce tun 1982 yake yin tiyata.

Ya bayyana cewa a lokacin da abokinsa Joseph Ugoh mai asibitin Gemanen Health Clinic ya kirasa ya buƙaci ya yi tiyatar, ya duba ya ga cewa Aneh na da ƙuraje kan ƙwayayenta haka kuma ƙwan haihuwarta na hannun dama ya kumbura.

Ya ce a lokacin da ya farka cikinta, ya kuma gano cewa tana da afendis wanda hakan ya sa ya tambayi abokinsa shawara kan cewa gwara ya cire saboda nan gaba kada ya rinƙa damunta.

Daga nan ne suka yi tiyatar kuma tun daga lokacin, babu wanda ya tuntuɓe shi ya ce ma shi akwai matsala da tiyatar da ya yi sai watan Fabrairu a lokacin da ƴan sanda suka je suka kama shi inda suka ce masa ya yi tiyata kuma ya cire wa wata ƙwayayen haihuwa.

Ya bayyana cewa ya yi aiki a asibitin Nyom tsawon shekara 12 kuma ya yi wa mutane da dama tiyata kuma ya ajiye aiki a asibitin inda ya kafa nasa kuma a cewarsa ya yi wa mutane da dama tiyata kuma babu wanda ya taɓa zuwa ya ce ya samu matsala irin haka.

Binciken ƴan sanda

Mai magana da yawun ƴan sanda reshen Jihar Benue Catherin Anene ta bayyana cewa ƴan sanda za su yi amfani da ƙwararru a wurin bincike haka kuma za su kai su kotu.

Haka kuma kwamishinan lafiya na Jihar Benue, Joseph Ngbea ya ce ya damu bayan samun labarin abin da ya faru.

Kwamishinan ya bayyana cewa a duk wata idan mace tana al'ada, ƙwayayen haihuwarta suna kumbura, sakamakon Kwende bai da ilimi kan jikin bil adama sai ya yi tunanin cewa ƙurji ne na ƙwayayen mahaifa.

Ya ce aikin ma'aikacin ɗakin tiyata ba wai aiki bane na yin tiyata, aikinsa shi ne ya taimaka wa likita a wurin tiyata da kayan aiki da kuma tabbatar da cewa an tsaftace su.

Ya ce gwamnatin jihar na da kwamiti na musamman wanda ke ƙunshe da jami'an tsaro da hukumar tattara haraji ta jihar inda suke ƙoƙrin gano asibitocin da ba su da rajista.

Ya bayyana cewa za su tabbatar da duk wanda ba shi da lasisi a jihar sun kama shi.