Damuwar da mutane ke nunawa kan biyan kudin haya na shekara a Lagos

Hoton wasu iyalai a gidansu

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Victor Ezeama
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos

Samun matsuguni mai kyau babban ƙalubale ne a ko'ina, amma haɗa kuɗin haya na shekara guda kafin a ba ka gidan ƙarin nauyi ne ga miliyoyin ƴan Najeriya.

Masu gidajen haya sun fi son a ba su kuɗin hayan a dunkule saboda yana rage yiwuwar gazawar ɗan haya wajen biyan kuɗin haya. A ganinsu, gara a matsa wa ɗan haya sau daya a shekara maimakon sau 12, wato kowane wata ke nan cikin shekara.

Sai dai da alama wannan tsarin ya kusa zuwa karshe.

Majalisun kasa a Abuja babban birnin Najeriya na kokarin kafa wata doka da za ta haramta karɓar kuɗin haya na shekara guda gabanin a bayar da hayar gidaje a kasar. A Legas babban birnin kasuwanci na ƙasar, hukumomi sun fara aiwatar da wani tsari na sa-kai da zai fara aiki daga watan gobe.

Gwamnatin jihar ta Legas na fatan cewa masu gidajen haya za su fi amincewa su karɓi kuɗin haya daga wata zuwa wata idan suka ga hukumomi sun shiga tsakaninsu da ƴan hayar.

Yawancin mazauna birnin, musamman matasa masu son yin aure nan kusa sun yaba da wannan tsarin na biyan kuɗin haya na wata-wata.

Tunde Omotayo wanda ke shirin yin aure a watan Afrilu na fuskantar jan aikin haɗa naira 600,000 zuwa naira 800,000 (wato $1,500-$2,000) domin ya biya kuɗin hayar wani gida a cikin birnin Legas.

Ga mutumin da albashinsa na wata bai wuce naira 300,000 ba, wannan jan aiki ne.

"Na yi tsammanin albashina zai iya ɗaukar nauyin kuɗi hayar da zan riƙa biya, sai dai na sha mamaki matuƙa. A halin yanzu zan so in riƙa biyan kuɗin haya daga wata zuwa wata saboda a halin yanzu na shiga cikin damuwa sosai."

Idan ya sami shiga cikin wannan sabon tsarin, zai riƙa biyan naira 50,000 a kowane wata ke nan, wanda yayi amanna zai sauwaƙa ma sa rayuwa tun da yana son yin aure nan ba da jimawa ba.

Gidaje sun fiye tsada a Legas

A matsayin ɗaya daga cikin birane mafi saurin bunkasa, kuɗin haya na karuwa a kowace rana kuma gidaje sun fiye tsada.

Ana karɓar gidaje masu ɗakin kwana biyu a yankin da ke kusa da cibiyar kasuwancin birnin wato Victoria Island kan dala( 4577540 )11,000 zuwa dala 22,000 (9155080) a shekara, inda gidaje masu sauƙi na kai wa tsakani dala 500 zuwa 5,000 (208070-2080700)a yankunan da ke da nisa daga nan.

A man rides a bicycle past a block of flats

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai 'yan Najeriya masu abin hannunsu da ke ficewa daga kwaryar birnin Legas zuwa irin wadannan tsararrun unguwannin a jihar Ogun mai makwabtaka inda kudin haya yafi sauki

Ya rage ga 'yan haya su nemo kudin da za su biya masu gidaje, kuma wannan ya tilastawa yawancin ma'aikata 'yan Najeriya bin wasu hanyoyi domin hada kan kudin haya daga cikin albashinsu na wata.

Wasunsu na karbar basussuka daga kamfanonin bayar da bashi - wadanda ke karbar kudin ruwan da ya kai kashi 28 cikin 100 a kowane wata, inda wasu kalilan cikinsu ke samun damar karbar bashi maras kudin ruwa daga wuraren da suke aiki domin su biya kudin hayan gidajen da suke son shiga.

Sai dai akwai masu gidajen hayan da ba su rungumi wannan sabon tsarin na biyan kuɗin haya daga wata zuwa wata.

Tosin Emmanuel, wani dan kasuwa a Legas ya ce wani mai gidan hayan da ya je wajensa ya soki tsarin.

"Mai gidan ya tambaye ni ko gwamnati ce ta sayo filin kuma ta gina gidan masa. Ya kuma ce babu gwamnatin da za ta tankwara shi kan yadda yake karɓar kudin hayan gidajensa."

Mista Emmanuel ya kuma ce "Mai gidan ya ce sai in tafi wajen gwamna Sanwo-Olu ya bani gida".

'Yan Najeriya sun saba da biyan kudi gabanin su shiga gidajen haya

Suna gina gidajen da suke so, kuma suna yin cajin kudin hayan da suke so a wannan bangare da kawo yanzu gwamnati ba ta sa ido a kai ba sosai.

Sai dai akwai 'yan haya masu yawa da ba sa son sauya wannan tsarin saboda sun riga sun sami mafaka kuma sun saba da tsohon tsarin.

'Yan Najeriya sun saba da biyan kudin kayayyaki baki daya gabanin su mallake su; misali motoci da wayoyin hannu da kudin makarantar 'ya'yansu.

Adaobi Asuoha

Asalin hoton, Adaobi Asuoha

Bayanan hoto, Yawancin 'yan Najeriya kamar Mrs Asuoha sun fi son biyan kudin haya gabanin su shiga gida domin "sauki ne"

Madam Adaobi Asuoha da ke zama a gundumar Ajah ta tsibirin Legas ta fi son ta biya kudin hayan gidan da ta ke zaune da iyalanta daga shekara zuwa shekara saboda tafi samun sauki da natsuwa na sauran watannin shekarar.

Ita ma kan ta gwamnatin jihar Legas ta gane cewa shirin nata na biyan kudin haya daga wata zuwa wata na hannun wadannan masu gidajen hayan ne da ke da karfin fada a ji, kuma sai yadda suka so za a yi.

"Mun san cewa a gwamnatance ba za mu iya tilasta wa masu gidajen haya su karbi kudaden daga wata zuwa wata ba," inji Toke Benson-Awoyinka, wani mai ba gwamnan Jihar Legas shawara kan harkokin muhalli.

Sai dai gwamnati ta ce an samar da sabo tsarin ne bayan tuntubar da ta yi da masu ruwa da tsaki kuma babu dalilin da zai sa shirin ya ki aiki.